Masarautar Benin

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Masarautar Benin


Wuri
Map
 10°N 10°E / 10°N 10°E / 10; 10

Babban birni Kazaure
Bayanan tarihi
Ƙirƙira 1170
Rushewa 1897
Mutum mutumin wani daga cikin sarakunan Benin
hotunan masarautar bennin

Masarautar Benin, wacce kuma ake kira daular Edo, ko kuma daular Benin (Bini: Arriọba ɗo ) wata masarauta ce a yankin kudancin Najeriya a yanzu.[1] Ba ta da dangantaka ta tarihi da jamhuriyar Benin ta zamani,[2] wacce aka fi sani da Dahomey daga karni na 17 har zuwa shekara ta 1975. Masarautar Benin babban birnin jihar ita ce Edo, wacce a yanzu ake kiranta da birnin Benin a jihar Edo, Najeriya. Masarautar Benin ta kasance "ɗaya daga cikin tsofaffin jihohin da suka fi ci gaba a gabar tekun yammacin Afirka". Ta girma ne daga Masarautar Edo da ta gabata ta Igodomigodo a wajajen karni na 11 miladiyya, [3] kuma ta daɗe har zuwa lokacin da Daular Burtaniya ta mamaye ta a shekarar 1897.

Oral traditions[gyara sashe | gyara masomin]

wasu daga cikin kayan yaƙe-yaken masarautar Benin

Asalin mutanen da suka kafa Masarautar Benin, ’yan ƙabilar Edo, tun farko su ne Ogiso (King's of sky) suka yi wa ƙasarsu suna Igodomigodo.[4] Ogiso na farko (Ogiso Igodo), ya yi tasiri sosai kuma ya samu farin jini a matsayinsa na shugaba nagari. Ya rasu bayan ya dade yana mulki sai Ere, babban ɗansa ya gaje shi. A cikin karni na 12, wani babban makircin faɗa ya barke kuma aka yanke wa yarima Ekaladerhan, ɗan ɗaya tilo na Ogiso na karshe hukuncin kisa, sakamakon sauya sakon baka ga Ogiso.[5] A cikin aiwatar da umarnin sarki na cewa a kashe shi, manzannin fadar sun yi jinƙai suka 'yantar da yariman a Ughoton kusa da Benin. Lokacin da mahaifinsa Ogiso ya rasu, sai daular Ogiso ta kare. Jama'a da sarakunan sarauta sun gwammace ɗan sarkinsu marigayi a matsayin wanda, zai gaje shi.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Bradbury, R. E. (16 August 2018), "Continuities and Discontinuities in Pre-colonial and Colonial Benin Politics (1897–1951)", Benin Studies, Routledge, pp. 76–128, doi:10.4324/9781351031264-4, ISBN 978-1-351-03126-4, S2CID 159119713, retrieved 27 January 2023
  2. "The kingdom of Benin". BBC Bitesize. Retrieved 19 December 2022.
  3. Strayer 2013.
  4. "The kingdom of Benin". BBC Bitesize. Retrieved 24 January 2023.
  5. "Benin Empire". motleytravels.org. Retrieved 9 July 2021.