Ifelodun (Kwara)
Appearance
Ifelodun | ||||
---|---|---|---|---|
| ||||
Wuri | ||||
| ||||
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya | |||
Jiha | Kwara | |||
Labarin ƙasa | ||||
Yawan fili | 3,435 km² | |||
Wasu abun | ||||
| ||||
Yanar gizo | ifelodunkwara.org.ng |
Ifelodun ƙaramar hukuma ce dake a jihar Kwara, Nijeriya. Cibiyar ta na nan a birnin Share.[1]
Mutanen garin Ifelodun yawancinsu Yarbawa ne kuma mafi asalin sh daga tsatson Igbomina da suke zaune a Ife, Oyo da kuma Ketu. An mamaye mafi akasarin yankin Igbomina a zamanin Afonja/Alimi kuma an hade ta a yankin Ilorin na yanzu.
Tana da fadin murabba’i 3,435 km2 da yawan jama’a kimanin mutum 206,042 dangane da kidayar shekara ta 2006.
Lambobin tura sako na yankin sune 241.[2] Tana dauke da akalla kauyuka da birane 80.
Addinai
[gyara sashe | gyara masomin]Akwai muhimman addinai guda uku a yankin:
- Musulunci
- Kiristanci
- Da wasu (Ifa, Sango, Elegun/Masqurade, Opele da dau sauran su).
Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Ifelodun Local Government Area". Kwara State Government. Archived from the original on 6 May 2014. Retrieved 8 September 2014.
- ↑ "Post Offices- with map of LGA". NIPOST. Archived from the original on 2009-10-07. Retrieved 2009-10-20.