Isa Mohammed Bagudu

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Isa Mohammed Bagudu
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

29 Mayu 1999 - 29 Mayu 2007 - Zainab Abdulkadir Kure
District: Gundumar Sanatan Neja ta Kudu
Rayuwa
Cikakken suna Isa Mohammed
Haihuwa 1948
ƙasa Najeriya
Mutuwa 5 Mayu 2007
Karatu
Harsuna Turanci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa Peoples Democratic Party

Isa Mohammed Bagudu (an haife shi a shekarar 1948) ɗan siyasan Nijeriya ne wanda aka zaɓa zuwa Majalisar Dattawan Nijeriya don ya wakilci yankin Neja ta Kudu a watan Afrilun 1999, kuma aka sake zaɓen sa a watan Afrilun 2003.

Tarihin Rayuwa[gyara sashe | gyara masomin]

An haife shi a shekarar 1948 na asalin Nupe, mahaifinsa Waziri Bagudu ya kasance memba na Hukumar Kula da Karamar Hukumar ta Ibadan a cikin shekarun 1950. Bagudu ya halarci kwalejin Ansarudeen, Isolo. Ya kasance darakta a NICON daga 1991 zuwa 1993.

Harkar Siyasa[gyara sashe | gyara masomin]

An zabi Bagudu ne a mazabar dan majalisar dattijan Neja ta Kudu ta jihar Neja a karkashin jam'iyyar PDP a watan Afrilun 1999 a farkon Jamhuriya ta Hudu ta Najeriya . An nada shi mataimakin shugaban kwamitin asusun ajiyar jama'a a watan Oktoba na shekarata 2004, yayi ƙaurin suna sosai a lokacin da ya mari 'yar uwansa sanata Mrs Iyabo Anisulowo, shugabar kwamitin Majalisar Dattawa kan harkokin Jiha da Kananan Hukumomi, a wajen zauren Majalisar Tarayya. A lokacin faruwar lamarin jaridar Guardian ta ruwaito cewa rikicin nasu na iya kasancewa yana da nasaba ne da fitar da kudaden kwamitin. Sakamakon hakan Majalisar Dattawa ta dakatar da shi na tsawon makonni biyu.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]