Jump to content

Ismael Nery

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Ismael Nery
Rayuwa
Haihuwa Belém, 9 Oktoba 1900
ƙasa Brazil
Mutuwa Rio de Janeiro, 6 ga Afirilu, 1934
Yanayin mutuwa Sababi na ainihi (Tarin fuka)
Ƴan uwa
Abokiyar zama Adalgisa Nery (en) Fassara  (1922 -
Karatu
Makaranta Académie Julian (en) Fassara
Escola Nacional de Belas Artes (en) Fassara
Harsuna Portuguese language
Sana'a
Sana'a painter (en) Fassara da Masanin gine-gine da zane
Hoton Nery.

Isma'il Nery (an haifeshi ne a ranar 9 ga watan Oktoba, shekarata alif 1900 zuwa ranar 6 ga watan Afrilu, shekarar alif 1934) mai zane ne ɗan kasar Brazil.

Tarihin Rayuwa

[gyara sashe | gyara masomin]

An haife shi a Belém, Pará na Dutch, san-asalin Brazil, da Afurka. Yayi karatu a Escola Nacional de Belas Artes (Makarantar Kasa ta Zane) da ke Birnin Rio de Janeiro sai kuma makarantar Académie Julian da ke Paris. Yayi zanuka da dama, kuma yayi wake da yawa sannan ya taimaka wajen zana Ginin Gado ta Kasar Brazil dake Sashin Baitulmalin kasar. Nery ya auri mawakiya Adalgisa Nery a shekarar 1922. Ya kamu da Tarin fuka a shekara ta 1931, sannan ya mutu a shekarar 1934. Aikin shi na musamman shine Autorretrato, 1927 (Autorretrato Rio/Paris), zanen da ake alakanta shi da zanen Green Violinist na Marc Chagall. A yau, MASP Autorretrato, 1927 (Autorretrato Rio/Paris) suna tallan shi.

An haifi Nery a 1900, sannan dangin shi zun zauna a Rio de Janeiro a shekarar 1909. A shekarar 1915, shiga Makarantar Zane ta Kasa. Ya yi kaura zuwa Turai a shekarar 1920, kuma ya halarci makarantar Académie Julian da ke Paris. A can gida, yayi aiki da sashin zane ta Cibiyar Asali ta Kasa dake karkashin Ma'aikatar Kudi, inda yayi abota da mawakiya Murilo Mendes. A 1922, ya auri Adalgisa Ferreira. A wannan lokacin yayi zanuka da salon zane na expressionists.[1][2]

Jigogin zanensa na musamman sau da yawa sun shafi mutane ne; zanen fuska, zanen fuskarsa, ko kuma tsiraici. Ba shida ra'ayin jigogin da suka shafi kasarsa, ko asalinsa ko kuma ala'dun Brazil. Yana fadada manufofin sa. Ya kuma kasance kuma mai zane a nan take. A 1929, ya shirya nuni zanukansa guda biyu, a Belém da Rio de Janeiro. Bai ji dadi yawan mahalartan ba. Ya kuma fafata a nunin kungiya da aka gabatar a New York.[2]

Cuta da mutuwa

[gyara sashe | gyara masomin]

A cikin wannan shekara ta 1929, bayan tafiya zuwa Argentina da Uruguay, binciken lafiya ya nuna cewa yana dauke da cutar Tarin fuka, wanda hakan ya tilasta masa rayuwa a killace na tsawo shekaru biyu. Yakan fito tsaf, a wasu lokutan kuma ya shiga wasu 'yan shirarun shirye-shirye kamar irin su Salão Revolucionário da aka gabatar a Rio de Janeiro as shekarar 1931 da kuma Exposição de Arte Moderna da SPAM a São Paulo a shekarar 1933. Amma a shekarar 1933, cutarsa ta dawo sosai, ya mutu a 1934 a lokacin yana da shekaru 33 a Rio de Janeiro. An birne shi a Franciscan, a gidan bauta na addininsa na Katolika.[2]

Abubuwan da ya bari

[gyara sashe | gyara masomin]

A shekarar 1959, Adalgisa Nery ta wallafa wani littafin nobel na tarihin rayuwarsa mai suna A Imaginária wanda ya zamo litttafin da akafi sayarwa. Littafin ya ta'allaka ne akan shekarun rayuwa da Ismael Nery. Adalgisa ta bayyana kewar da taji daga farko game da mijinta, amma kuma a dangantaka mai cike da hanguza, cutarwar zuciya da ke tattare da Ismael Nery, da kuma rikicinta na rayuwar yau da kullum.[3]

Mutane da masu suka sun mance da ayyukan Ismael Nery, har zuwa shekarun 1960s, a lokacin da aka zana zunansa a Bikin zanen Biennale na São Paulo, a wani daki da aka sadaukar wa masu zane na musamman. An kuma nuna ayyukansa a wurin Taron Bikin Zane na Kasa da Kasa (Biennalle) na goma.

A cikin shekarun 1966 a Birnin Rio de Janeiro, da kuma a alif 1984, Gidan Tarihin Zanen na Zamunan Baya na Jami'ar São Paulo (Tunawa da Ismael Nery - bayan shekaru 50), anyi bukukuwan tunawa da ayyukansa har sau biyu.

  1. Quint, Anne-Marie (2002). Escrevo-lhe (in Faransanci). Presses Sorbonne Nouvelle. ISBN 978-2-87854-246-2.
  2. 2.0 2.1 2.2 Cultural, Instituto Itaú. "Ismael Nery". Enciclopédia Itaú Cultural (in Harshen Potugis). Retrieved 2020-05-13.
  3. www.sescsp.org.br https://www.sescsp.org.br/online/artigo/compartilhar/3106_A+LUTA+DE+DUAS+ESCRITORAS+PARA+VENCER+O+PRECONCEITO. Retrieved 2020-05-13. Missing or empty |title= (help)