Adalgisa Nery
Adalgisa Nery | |||
---|---|---|---|
| |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Rio de Janeiro, 29 Oktoba 1905 | ||
ƙasa | Brazil | ||
Harshen uwa | Portuguese language | ||
Mutuwa | Rio de Janeiro, 7 ga Yuni, 1980 | ||
Yanayin mutuwa | Sababi na ainihi (Bugun jini) | ||
Ƴan uwa | |||
Abokiyar zama |
Ismael Nery (en) (1922 - Lourival Fontes (en) (1940 - | ||
Karatu | |||
Harsuna | Portuguese language | ||
Sana'a | |||
Sana'a | maiwaƙe, ɗan jarida, ɗan siyasa, marubuci, Mai wanzar da zaman lafiya da Marubuci | ||
Kyaututtuka | |||
Imani | |||
Jam'iyar siyasa |
Brazilian Socialist Party (en) Brazilian Democratic Movement (en) |
Adalgisa Nery (ta rayu a tsakanin 29 ga watan Oktoban 1905 zuwa ranar 7 ga watan Yuni, shekara ta alif 1980) mawakiya ce 'yar Brazil, ''yar jarida kuma ''yar siyasa.
Tarihin Rayuwa
[gyara sashe | gyara masomin]An haife ta a Birnin Rio de Janeiro da suna Adalgisa Maria Feliciana Noel Cancela Ferreira, 'ya ce ga wani ma'aikacin farar hula. A 1922, sunyi aure da Ismael Nery (1900–1934),[1] mai zane kuma mawaki wanda ya gabatar da Adalgisa ga dumbin masu zanen kasar Brazil da masu hikima, irin su Manuel Bandeira, Jorge de Lima da kuma Murilo Mendes. Su biyun sun rayu a Turai a tsakanin shekarun 1927 zuwa 1929, inda suka hadu da mai zane Marc Chagall da kuma marubucin wakoki dan Brazil, Heitor Villa-Lobos. Mijinta Ismael ya mutu ta sanadiyyar cutar tarin fuka a shekarar 1934, kuma ya bar Algaisa da 'ya'ya maza biyu.[1]
Adalgisa ta fara da wallafa wakoki da tatsuniyoyi bayan mutuwar mijinta na farko, littafinta na farko mai suna Poemas, wanda aka wallafa a 1937, ya samu karbuwa a wajen masu suka, sannan kuma ta rubuta gajerun labarai da kuma labarun mujallu. Duk da cewa mawaki Murilo Mendes ya neme ta da aure a karshen shekarun 1930s, tayi aure a 1940 da Lourival Fontes (1899–1967), darekta janar na Sashin Labarai da Farfaganda (DIP). DIP suke da alhakin kula da sahihancin rubuce-rubuce. Adalgisa ta taimakawa DIP a matsayin darektan zamantake sannan kuma jami'ar hulda da jama. A lokacin da aka nada Fontes a matsayin Jakadan Kasar Brazil a Mexico a shekarar 1944, Adalgisa ta raka shi inda ta hadu da Diego Rivera (wanda yayi zanen fuskokin Adalgisa), da Frida Kahlo, José Clemente Orozco da kuma David Alfaro Siqueiros.
Bayan Adalgisa da Fontes sun rabu a shekarar 1953, Adalgisa ta fara harkokin siyasa a rayuwar ta. A matsayinta na marubuciyar insha'i ga gidan jaridar Rio de Janeiro daga Última Hora, ta yi goyi bayan gurguzanci da kuma 'yancin kasar Brazil. Nasarar da rubutun jaridar da Nery tayi ya taimaki Adalgisa a wajen zabenta a matsayin mamba na majalisar mazabar Guanabara (a yanzu birni ne a karkashin Rio de Janeiro) a shekarar alif 1960 a karkashin Jam'iyyar Gurguzanci na Kasar Brazil (PSB). Adalgisa ta bambanta kanta a majalisa a sanadiyyar adawa da gwamnan Guanabara Carlos Lacerda da kuma tsananin rike gaskiyar ta. An sake zabarta a majalisa a alif 1962 da kuma 1966. Bayan Mulkin Soja ya haramta jam'iyyun siyasa a shekarar 1965, Adalgisa ta shiga Kuniyar 'Yancin Kasar Brazil [Brazilian Democratic Movement (MDB)] wanda suka zamo kungiyar adawa a hukumance da mulkin soja. A cikin shekarar 1969, Gwamnatin Soja da ke mulkar kasar Brazil a lokacin ta kawo karshen aikin Adalgisa, kuma sun kwace duk wata alfarma a gare ta na aiki a ofis ko kuma a zabe ta na tsawon shekaru goma.[2]
Adalgisa ta kwashe sauran rayuwarta a cikin bakin ciki da kadaici. Ta mutu a wani gidan gajiyayyu a Rio de Janeiro.
An fassara gajerun labaranta da dama zuwa harsunan Turanci, Faransanci, Jamusanci, da kuma Italiyanci.
Ayyukanta
[gyara sashe | gyara masomin]- Poemas 1937
- A mulher ausente (wakoki) 1940
- Og (short stories) 1943
- Ar do deserto (wakoki) 1943
- Cantas de angústia (wakoki) 1948
- As fronteiras da quarta dimensão (poems) 1952
- A imaginária (nobel) 1959
- Mundos oscilantes (poems) 1962
- Retrato sem retoque (tarin rubuce-rubucen jarida) 1966
- 22 menos 1 (gajerun labarai) 1972
- Neblina (nobel) 1972
- Erosão (wakoki) 1973
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ 1.0 1.1 Darlene J. Sadlier (22 February 1992). One Hundred Years after Tomorrow: Brazilian Women's Fiction in the Twentieth Century. Indiana University Press. pp. 140–. ISBN 0-253-11569-8. Retrieved 19 April 2020.
- ↑ Alzira Miranda (3 November 2010). "Adalgisa Nery (por Alzira Miranda) Diversão - Memória" (in Harshen Potugis). Retrieved 21 July 2011.[dead link]