Itu

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Itu kungiya ce a karamar hukumar Ezinihitte Mbaise a jihar Imo. Yawancin mutane suna kiransa da Itu Mbaise. Domin akwai wani gari da ake kira Itu a jihar Kuros Riba. Itu gari ne da ya shahara wajen sana'arnoman dabino da kuma noma. A siyasance, ita ce zuciyar karamar hukumar Ezinihitte tunda tana da hedikwatar karamar hukumar dake Itu. Itu birni ne mai ƙauye 10, kuma wani lokaci ana kiransa “Itu Ama iri”, saboda ƙauyuka 10 da suka haɗa da Itu.