Jump to content

Jae Deen

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jae Deen
Rayuwa
Haihuwa Ontario (mul) Fassara, 23 Satumba 1994 (30 shekaru)
Karatu
Makaranta Carleton University (en) Fassara
Sana'a
Sana'a mawaƙi
Artistic movement hip hop music (en) Fassara
Imani
Addini Musulunci

Sheikh Jamal ada an sanshi da Joshua Asare , Mawaki ne ɗan asalin ƙasar Ghana da Kanada a wakar salon gambarar zamani wato HIP HOP da R&B. Yafara tashe ne daga fitar da rimis na shahararrun wakokin sa a shafukan sadar da zumunta. Deen mamba ne a ƙungiyar Deen Squad, ƙungiyar dake fitar da wakokin addinin Musulunci na salon Hip Hop.

Farkon rayuwar sa

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Jae Deen a birnin Ottawa, Ontariyo. Sunan sa na haihuwa shine Joshua Asare. Ya musulunta daga Kiristanci yana dan shekara 15. Jae ya fara rubutawa da buga wakokin salon Rap da abokan sa a lokacin yana makaran ta.

Nasarorin sa

[gyara sashe | gyara masomin]

Ya samu kyautar RIS (Reviving the Islamic Spirit) a 2013 ya zama "na 16" a duniyar kungiyar mawaka ta Awakening Records’ sai "Worldwide Talent Contest". A 2015, ya hade da gamaiyar mawaka ta Ampli-Tune Records for management and representation