Jump to content

Jagun Jagun (Fíìmù Nàìjíŕà)

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jagun Jagun
Furuci Jagun jagun
Dan kasan Nigeria
Gama mulki Femi adebayo
Organisation Faithia Balogun

Jagun Jagun fim ne mai ban sha'awa wanda Netflix ya fitar a cikin shekara ta alif dubu biyu da Ashirin da uku 2023. Fim ne na wasan kwaikwayo, wanda Femi Adébayo da Euphoria360 Media suka shirya. Adebayo Tijani da Tope Adebayo Salami sune daraktocin wasan. Daga cikin mahalarta taron akwai Femi Adebayo, Lateef Adédiméji, Bimbo Ademoye, Faithia Balogun, Mr Macaroni, Bukunmi Oluwashina, Ibrahim Yekini da Muyiwa Ademola . Netflix ya fitar da nunin a ranar goma 10 ga watan Agusta, shekara ta alif dubu biyu da ashirin da uku 2023, don kallo.[1]

Mahallin tarihi

[gyara sashe | gyara masomin]

Fim din Jagun Jagun ya samo asali ne daga labarin wani jarumi mai suna Ogundiji. Wannan jarumin yana da karfi, shahararre ne, kuma yana jawo tsoro ga garuruwan yankinsa, amma karfin wani matashi mai suna Obutija da ya zo horo domin daukar fansar mahaifinsa ya fara tsorata shi. Tunda yankin Ogundiji ya kasance ‘yan mulkin mallaka kuma ya samu nasarori da dama wajen karbe garin don ba wa shugabannin da ba su dace ba. Shigowar Abbottija da sauri ya ba shi tsoro, ya fara laluben hanyoyi daban-daban don fitar da shi daga hanya.

Fim din Jagun Jagun an yi shi ne a yammacin Najeriya, kuma an kwashe sama da wata guda ana fitar da shi. Wata ‘yar fim mai suna Bukunmi Oluwashina ta bayyana cewa Femi Adebayo ya zabe ta ne a kan labarin da ya yi shekara daya da ta wuce, kafin a fara aikin fim din.

Femi Adebayo, wanda ya shirya fim din ya tabbatar da cewa aniyarsa ita ce ya sa fim din Jagun Jagun ya samu nasara fiye da wadanda ya yi a baya, har ma fiye da Sarkin barayi .

A ranar goma 10 ga watan Agusta (Agusta 10), shekarar alif dubu biyu da ashirin da uku 2023, an fitar da fim ɗin Jagun Jagun akan Netflix. A cikin sa'o'i arba'in da takwas 48 da sakin ta, ta fara yaduwa a cikin Burtaniya da wasu kasashe goma sha bakwai 17. A cikin kwanaki uku da fitowar fim din, mutane miliyan biyu da dubu ɗari[2]2,100,000 ne suka kalli fim din, kuma a karshen kwanaki ashirin 20, watan Agusta, shekara ta alif dubu biyu da ashirin da uku 2023, mutane miliyan ukku da dubu ɗari bakwai 3,700,000 ne suka kalli fim din. Wannan ya sa ya zama ɗaya daga cikin manyan fina-finai goma 10 da aka fi kallo.[3]

  1. https://www.pulse.ng/entertainment/movies/here-is-your-first-look-at-netflixs-jagun-jagun/2qg35f1
  2. Afigbo, Chinasa (2023-08-12). ""Record-breaking": Femi Adebayo's new film hits top 10 in 18 countries in 48 hrs". Legit.ng - Nigeria news. (in Turanci). Retrieved 2023-08-12.
  3. Netflix. "Weekly Top 10 lists of the most-watched TV and films" (in Turanci). Retrieved 2023-08-17.