Jana Fernández
Jana Fernández | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
Rayuwa | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Haihuwa | Martorell (en) , 18 ga Faburairu, 2002 (22 shekaru) | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
ƙasa | Ispaniya | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Karatu | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Harsuna | Yaren Sifen | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | ɗan wasan ƙwallon ƙafa | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
| |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Muƙami ko ƙwarewa | Mai buga baya | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Tsayi | 1.62 m |
Jana Fernández Velasco (anhaifeta ne a ranar 18 ga watan fabrairu a shekarar 2002),[1]ƙwararriyar 'yar wasan ƙwallon ƙafa ce ta ƙasar Sipaniya wadda ke taka leda a matsayin 'yar wasa mai tsaron baya a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta FC Barcelona kuma jagora a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Spain ta U20.[2]
Aikin Kungiya[gyara sashe | gyara masomin]
An haifi Fernández a Martorell a garin Baix Llobregat a lardin Barcelona. Ta fara koyon kwallon kafa a La Masia ta FC Barcelona a shekarar 2014 tana 'yar shekaru 12.[3]
Fernández ta fara taka leda a Barcelona a watan Nuwamba a shekarar 2018.[4]
tana shekara 16 da watanni 9, yayin da take wasa da sashin Juvenil-Cadet na ƙungiyar. Ita ce 'yar wasa ta biyu mafi ƙarama a ƙungiyar bayan ƙwararrun FC Barcelona ta mata a cikin 2015.[5] A lokacin bazara na 2020, Fernández ta rattaba hannu kan kwantiraginta na farko na cikakken ƙungiyar na shekaru uku.
Aikin Kasa[gyara sashe | gyara masomin]
Fernández ta taka leda tare da dukkan kungiyoyin matasa na kasar Sipaniya, gami da U17, U19, da U20s.[6]
Ta kasance cikin tawagar 'yan kasa da shekara 17 ta kasar Sipaniya wacce ta lashe gasar cin kofin nahiyar Turai ta U-17 na shekarar 2018. Ta lashe gasar zakarun U-17, Spain ta cancanci shiga gasar cin kofin duniya ta U17 ta 2018 kai tsaye. Fernandez ta buga kowane wasa a kungiyar Spain da ta lashe gasar, gasar cin kofin duniya ta farko da matan Spain suka lashe a kowane fanni na shekaru.
Kididdigar Aiki[gyara sashe | gyara masomin]
Hotuna[gyara sashe | gyara masomin]
-
-
-
Jana tareda duk 'yan qungiyar ta
Nasarori[gyara sashe | gyara masomin]
•UEFA Women's Champions League : 2020–21 , 2022– 23 [12] •Primera División : 2020–21 , 2021–22 , 2022–23 •Copa de la Reina : 2020–21 •Supercopa de España Femenina: 2021–22 , 2022–23 •Spain U17 •U-17 European Championship: 2018 •U-17 World Cup: 2018
Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]
- ↑ https://en.m.wikipedia.org/wiki/Jana_Fernández
- ↑ https://www.fcbarcelona.com/en/football/womens-football/players/1736079/jana
- ↑ https://players.fcbarcelona.com/en/player/2803-jana-jana-fernandez
- ↑ https://www.besoccer.com/player/jana-fernandez-469944
- ↑ https://www.365scores.com/football/player/jana-fernandez-66199
- ↑ https://www.eurosport.com/football/jana-fernandez_prs517688/person.shtml