Jerin Jami'oin Najeriya
Appearance
Wannan shine jerin jami'o'in Najeriya . Najeriya tana da tsarin jihohi har guda 36 da kuma babban birnin tarayya . Sakamakon samuwar arzikin man fetur a shekarar alif 1970, an fadada matakin karatun manyan makarantu zuwa kowane yanki na kasar Najeriya. [1] [2] A baya gwamnatin tarayya da na jihohi su ne kawai hukumomin da aka ba wa lasisin gudanar da jami'o'i. Awani lokaci can baya, an fadada ba da lasisi ga daidaikun mutane, ƙungiyoyin jama'a da ƙungiyoyin addini don kafa jami'o'i masu zaman kansu a cikin ƙasar.
Hukumar Kula da Jami'o'i ta Kasa (NUC) ita ce babbar hukumar da take tabbatar da daidaito da kuma tsara damar shiga kowace jami'a a Najeriya.