Jibrin Ndagi Baba

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jibrin Ndagi Baba
Rayuwa
Haihuwa Jihar Neja, 1979 (44/45 shekaru)
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa

Jibrin Ndagi Baba (an haife shi a shekara ta 1979) ɗan siyasa ne kuma ɗan majalisar dokokin jihar Neja mai wakiltar mazaɓar Lavun a matakin majalisar dokokin jihar.[1] Ya gaji Bako Kasim Alfa a matsayin mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Neja bayan ya bayyana murabus ɗinsa a matsayin mataimakin kakakin bisa wasu dalilai da ba a bayyana ba.[2][3]

Gambo Sulaiman Rabiu mai wakiltar mazaɓar Paikoro ne ya zaɓe shi a matsayin magajin Bako Kasim Alfa, sannan Saleh Ibrahim Alhaji na Mazaɓar Kontagora II ya mara masa baya.[4][5]

Yuli 23, 2020 taron gama gari[gyara sashe | gyara masomin]

Jibrin Baba ya kasance a ranar 23 ga Yulin shekarar 2020 a zaman taron ranar alhamis, ya gabatar da ƙudirin tsige sabon shugaban masu rinjaye biyu da mataimakinsa na a tsige shi daga muƙamin saboda rashin ƙwarin gwiwa a matsayin mamba mai riƙe da muƙamai biyu.[6][7]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. https://www.shineyoureye.org/person/jibrin-ndagi-baba
  2. https://dailypost.ng/2020/07/23/breaking-niger-assembly-deputy-speaker-resigns/
  3. https://ab-tc.com/niger-state-assembly-deputy-speaker-resigns/
  4. https://ait.live/niger-state-house-of-assembly-elects-new-deputy-speaker/
  5. https://www.legit.ng/1350275-niger-assembly-deputy-speaker-resigns-elected.html
  6. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2021-05-20. Retrieved 2023-03-11.
  7. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2021-05-20. Retrieved 2021-05-20.