Jim Émilien Ngowet Allevinah (An haife shi a ranar 27 ga watan Fabrairu shekara ta 1995) ƙwararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne wanda ke taka leda a matsayin ɗan wasan tsakiya. Kulob din Clermont. An haife shi a Faransa, yana wakiltar Gabon a matakin kasa da kasa.[1]
An haife shi a Faransa, Allevinah ya zaba don wakiltar Gabon a babban matakin kasa da kasa. Ya buga wasansa na farko a duniya a ranar 23 ga Maris din shekarar 2019 da Burundi, inda ya fara da buga cikakken mintuna 90 na wasan da suka tashi 1-1, wanda ya kawar da Gabon daga shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka.[2][3]
A ranar 5 ga watan Satumba 2021, ya ci kwallonsa ta farko a wasan da suka tashi 1-1 da Masar a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya na FIFA.[4][5] Bayan watanni biyu, ya sake zura kwallo a ragar Masar a fafatawar da suka yi da Masar da ci 2-1.[6]
An zabi Allevinah ne a tawagar Gabon a gasar cin kofin Afrika ta 2021.[7] Ya buga dukkan wasanni ukun da Gabon ta buga a matakin rukuni, inda ya zura kwallo a bugun daga kai sai mai tsaron gida a ragar Ghana[8] da kuma kwallon farko da suka tashi kunnen doki da Morocco wanda hakan ya taimaka wa Gabon ta tsallake zuwa zagayen gaba.[9]
↑Donnarel, William (25 June 2019). "Football : d'Agen à la Ligue 2, l'incroyable ascension de Jim Allevinah" [Football: from Agen to Ligue 2, the
incredible rise of Jim Allevinah. Le Petit Bleu d'Agen (in French). Retrieved 25 June 2019.
↑Burundi v Gabon game report". Confederation of African Football. 23 March 2019. Archived from the original on 25 March 2019. Retrieved 23 March 2019.
↑Maurès, Sébastien (19 March 2019). "Football:
Jim Allevinah prêt à rugir face au Burundi" [Football:
Allevinah ready to roar against Burundi]. Sud Ouest
(in French). Retrieved 20 January 2022.
↑"Le bilan de nos internationaux" [The results of our internationals] (in French). Clermont Foot. 10
September 2021. Archived from the original on 16
September 2021. Retrieved 20 January 2022.
↑"L'Égypte, réduite à dix, arrache le match nul au Gabon en qualifications pour la Coupe du monde 2022" [Egypt, reduced to ten, snatch the draw in
Gabon in qualifying for the 2022 World Cup]. L'Équipe
(in French). Éditions Philippe Amaury. 5 September
2021. Retrieved 20 January 2022.
↑Le bilan de nos internationaux" [The results of our internationals] (in French). Clermont Foot. 19
November 2021. Archived from the original on 22
November 2021. Retrieved 20 January 2022.
↑Oludare, Shina (18 December 2021). "Afcon 2021: Arsenal's Aubameyang, Brighton's Ella headline Gabon provisional squad". Goal. Retrieved 20 January 2022.
↑Gleeson, Mark (14 January 2022). "Ghana held after late Gabon equaliser in feisty affair". Reuters.
Retrieved 20 January 2022.
↑Le Gabon se qualifie pour le prochain tour, avec un
match nul contre le Maroc" [Gabon qualifies for the next round, with a draw against Morocco.] (in French). Gabonese Football Federation. 19 January
2022. Retrieved 20 January 2022.