John Ssenseko Kulubya

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
John Ssenseko Kulubya
Rayuwa
Haihuwa Uganda, 1935
ƙasa Uganda
Mazauni Kampala
Mutuwa 27 ga Augusta, 2019
Yanayin mutuwa  (Ciwon huhu)
Karatu
Makaranta University of London (en) Fassara
King's College Budo (en) Fassara
Budo Junior School (en) Fassara
Makerere University (en) Fassara
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a injiniya, rally driver (en) Fassara da ɗan kasuwa

John Ssenseko Kulubya (1935 - 27 ga Agusta 2019), injiniya ne, ɗan kasuwa, kuma ɗan siyasa a Uganda.[1] An ruwaito shi a cikin 2012 yana daya daga cikin mafi arziki a Uganda.[1]

Tarihi da ilimi[gyara sashe | gyara masomin]

An haife shi a Uganda a kusan shekara ta 1935 (1934 bisa ga wasu kafofin). Mahaifinsa shi ne marigayi Sserwano Ssenseko Wofunira Kulubya (CBE), wanda ya zama magajin garin Kampala daga shekarun 1959 zuwa 1961, kuma shi ne magajin garin Afirka na farko a babban birnin Uganda. Mahaifiyarsa ita ce Uniya Namutebi.[2] Ya yi karatu a Buddo Junior School, Kings College Budo da makerere college da Kampala Technical School (wanda a yanzu ake kira Kyambogo Technical Institute) daga nan ya kammala karatunsa na kanikanci a shekarar 1952.[2] Matashin Kulubya ya samu horo a matsayin injiniya.[3][4]

Kasuwanci da zuba jari[gyara sashe | gyara masomin]

Kulubya ya mallaki gine-gine da filaye masu girman gaske a yankunan babban birnin Kampala da kuma wasu yankuna na yankin tsakiyar kasar Uganda.[3][5]

Aikin siyasa[gyara sashe | gyara masomin]

Ya tsaya takara, bai yi nasara ba a matsayin magajin garin Kampala, a 2006.[6][7]

Na sirri[gyara sashe | gyara masomin]

Sssenseko Kulubya ya yi aure kuma ya kasance uban yara hudu.[3]

Duba kuma[gyara sashe | gyara masomin]

  • Jerin mutane mafi arziki a Uganda

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. 1.0 1.1 Michael Kanaabi, and Ssebidde Kiryowa (6 January 2012). "The Deepest Pockets". New Vision. Kampala. Retrieved 11 March 2016.
  2. 2.0 2.1 "Ssenseko Kulubya : Omuddugavu eyasooka okumalako Safari Rally". www.bukedde.co.ug. 2015-03-17. Archived from the original on 27 August 2019. Retrieved 2019-08-27.
  3. 3.0 3.1 3.2 Hafsah Nabayunga, and Kelvin Nsangi (25 September 2007). "Kampala set to get new Mayor". Daily Monitor. Kampala. Archived from the original on 28 August 2018. Retrieved 11 March 2016.
  4. Walakira (9 August 2012). "Full list of past mayors of Kampala, first woman mayor of Kampala, first woman acting mayor of Kampala, long serving mayor of Kampala". Weinformers.net (WIN). Archived from the original on 12 March 2016. Retrieved 11 March 2016.
  5. Nalubwama, Jackie (29 October 2013). "Who owns Lugazi town?". The Observer. Kampala. Retrieved 11 March 2016.
  6. Vision Reporter (12 February 2006). "Kulubya put to task over president". New Vision. Kampala. Retrieved 11 March 2016.
  7. Vision Reporter (23 January 2006). "News in Brief". New Vision. Kampala. Retrieved 11 March 2016.