Jolly Nyame

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jolly Nyame
Gwamnan jahar Taraba

29 Mayu 1999 - 29 Mayu 2007
Bala Nuhu (en) Fassara - Danbaba Suntai
Gwamnan jahar Taraba

ga Janairu, 1992 - Nuwamba, 1993
Adeyemi Afolahan (en) Fassara - Yohanna Dickson
Rayuwa
Haihuwa Zing (Nijeriya), 25 Disamba 1955 (68 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Harsuna Turanci
Hausa
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa Peoples Democratic Party

Jolly Tavoro Nyame (an haife shi 25 Disamba 1955) a ƙaramar hukumar Zing ta jihar Taraba a yau ) shi ne gwamnan jihar Taraba a Najeriya daga 29 ga Mayu 1999 zuwa 29 ga Mayu 2007. Ya kuma yi gwamnan jihar daga watan Janairu 1992 zuwa Nuwamba 1993. Shi dan jam’iyyar PDP

Rayuwar farko[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Nyame a ranar 25 ga Disamba, 1955 a Zing, jihar Taraba. yayi aikin Firist kuma an nada shi Reverend a Cocin United Methodist Church of Nigeria.

Siyasa[gyara sashe | gyara masomin]

Nyame ya shiga siyasa ne a shekarar 1991, ya tsaya takarar gwamnan jihar Taraba a 1992 kuma ya yi nasara. Wa’adinsa na gwamna a shekarar 1992 bai dade ba sakamakon kwace mulki da sojoji suka yi. A 1999, Nyame ya tsaya takarar gwamna a jam’iyyar Peoples Democratic Party kuma ya yi nasara. An kuma sake zabe shi a shekarar 2003, wanda hakan ya sa ya zama mutum daya tilo da ya lashe zaben gwamna sau uku a jihar Taraba. [1]

Tuhumar laifuka[gyara sashe | gyara masomin]

Bayan da ya bar ofis a shekarar 2007, Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ta tuhumi Nyame da laifin zamba na Naira biliyan 1.64 a kan tuhume-tuhume arba’in da daya na zamba. A shekarar 2007, Nyame ya amince da karkatar da naira miliyan 180 daga cikin naira miliyan 250 da aka tanadar wa ma’aikatu a jihar Taraba, ya kuma yi tayin dawo da kudin. [1]

Hukunci[gyara sashe | gyara masomin]

A ranar 30 ga watan Mayun 2018 ne wata babbar kotun birnin tarayya Abuja ta yanke wa Nyame hukuncin daurin shekaru 14 a gidan yari, mai shari’a Adebukola Banjoko, bisa laifin da ake tuhumarsa da shi. An nemi ya mayar da kudaden da ya karkatar.

A watan Nuwamba 2018, Kotun daukaka kara da ke Abuja ta tabbatar da samunsa da laifuka 29. Sai dai kotun daukaka kara ta sake duba hukuncin da kotun ta yanke, ta kuma yanke masa hukuncin zaman gidan yari na shekaru 5 daban-daban na shekaru 12 da zai yi a lokaci guda maimakon zaman gidan yari na shekara 14 na farko sannan ta umarce shi da ya biya tarar naira miliyan 185. A ranar 7 ga Fabrairu, 2020, Kotun Koli ta tabbatar da hukuncin zaman gidan yari na shekaru 12 tare da jingine tarar da kotuna suka yi masa kan cewa sun yi taurin kai kuma sun aikata ba tare da wani dalili ba.

Afuwa[gyara sashe | gyara masomin]

A ranar 14 ga watan Afrilu ne gwamnatin tarayyar Najeriya tayiwa Joshua Dariye da Jolly Nyame afuwa. Kungiyoyin fararen hula da sauran jama'a sun soki matakin.

kebantacciyar Rayuwa[gyara sashe | gyara masomin]

Nyame yana auren Priscilla JT Nyame.

karin bayani[gyara sashe | gyara masomin]

  • Jerin Gwamnonin Jihar Taraba

manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. 1.0 1.1 Cite error: Invalid <ref> tag; no text was provided for refs named auto175

Template:TarabaStateGovernors