Josephine Ada Omaka ko kuna anfi saninta da suna Josephine Omaka (an haife shi 29 ga watan Nuwamba, shekarar 1993) yar' asalin Najeriya ce kuma mai wasar hanzari. Ta yi gasa a gasa a cikin gida da na kasa da kasa a wasannin guje-guje da wakilci a Najeriya.
Josephine Ada Omaka ta fara aikinta a matsayinta na yar tsere da gudu da sauri a Najeriya inda ta fafata a gasa daban-daban na gida. Ta lashe manyan lambobin zinare gwal a gasar wasannin guje-guje da tsalle-tsalle ta matasa ta shekarar 2011 da shekarar 2010 a wasannin guje-guje a tseren mita 100 sannan kuma ta shiga gasar tseren mita 4 × 100 a gasar guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya ta 2012 wacce aka gudanar a Estadi Olímpic Lluís Companys a 13 da 14 ga Yuli, ita ma ta lashe gasar Zakarun Afirka na Afirka na shekarar 2009 a cikin tseren mita 100 da kuma wani azurfa a gasar tseren gudun mita 4 * 100 na Najeriya a shekarar 2009 tare da Margaret Benson, Goodness Thomas da Wisdom Isoken . Bugu da kari, ta shiga cikin rukunin tseren gudun fanfalaki na 4 × 400 na Afirka wanda ya lashe lambobin zinare a gasar wasannin Olympics ta matasa ta shekarar 2010 tare da Nkiruka Florence Nwakwe, Izelle Neuhoff da Bukola Abogunloko .