Josephine Piyo
2023 - | |||
| Rayuwa | |||
| Haihuwa | Barkin Ladi, 13 Satumba 1957 (68 shekaru) | ||
| ƙasa | Najeriya | ||
| Karatu | |||
| Harsuna |
Turanci Pidgin na Najeriya | ||
| Sana'a | |||
| Sana'a |
ɗan siyasa, nurse (en) | ||
| Imani | |||
| Addini | Kiristanci | ||
| Jam'iyar siyasa | Peoples Democratic Party | ||
Josephine Chundung Piyo (an haife ta a shekara ta 1957) ƴar siyasar Najeriya ce wadda ta take riƙe muƙamin mataimakiyar gwamnan jihar Filato a halin yanzu.[1][2] Kafin ta zamo mataimakiyar Gwamnan jihar Filato, an zaɓeta a matsayin ƴar Majalisa a Majalisar dDokoki ta Jihar Filato.
Tasowa
[gyara sashe | gyara masomin]Piyo ta fito ne daga ƙaramar hukumar Barkin Ladi, An haife ta a shekara ta 1957. Haifaffiyar garin Barkin Ladi, Jihar Filato.
Aiki
[gyara sashe | gyara masomin]Tayi aiki a matsayin ma'aikaciyar jinya, haka ita Malama ce kafin ta shiga harkar siyasa. A cikin shekara ta1999 an zaɓe ta a matsayin ƴar Majalisar Dokokin Jihar Filato. Piyo ta riƙe matsayin mai ba gwamnan jihar Filato shawara ta musamman, daga shekara ta 2008 zuwa 2011. Har ila yau a cikin shekara ta 2018, ta zama shugabar ƙaramar hukumar Riyom, jihar Filato.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "2023: Plateau PDP Guber Candidate Picks Female Running Mate – This Day Live". thisdaylive.com. Retrieved 2023-04-19.
- ↑ YarKarkara, Sawabiya (2022-06-21). "Plateau Governorship:Mutfwang picks a Female Lawmaker of the 4th Assembly as Running Mate". Sawabiya News. Archived from the original on 2023-04-19. Retrieved 2023-04-19.