Julian Brandt
Julian Brandt | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
Rayuwa | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Haihuwa | Bremen, 2 Mayu 1996 (28 shekaru) | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
ƙasa | Jamus | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Harshen uwa | Jamusanci | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Karatu | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Harsuna | Jamusanci | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | ɗan wasan ƙwallon ƙafa | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
| |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Muƙami ko ƙwarewa |
wing half (en) attacking midfielder (en) | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Lamban wasa | 19 | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Nauyi | 82 kg | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Tsayi | 185 cm |
Julian Brandt ƙwararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne na ƙasar Jamus wanda ke taka leda a matsayin ɗan wasan gefe ko kuma na tsakiya mai kai hari ga ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Borussia Dortmund da kuma ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta ƙasa ta Jamus.[1]
Brandt ya buga wasanni sama da 55 a jumulla da ƙungiyoyin matasan Jamus, yana wasa a kowane mataki daga U15 zuwa U21.[2] Ya kasance memba a cikin tawagar da ta lashe gasar cin kofin nahiyar Turai ta 'yan ƙasa da shekaru 19 a 2014.[3][4]
Sana'ar Kungiya
[gyara sashe | gyara masomin]Julian Brandt an haife shi kuma ya girma a Bremen. A lokacin matashi, ya taka leda a garinsu a ƙungiyar SC Borgfeld sannan a ƙungiyar FC Oberneuland kafin ya shiga makarantar matasa ta (Nachwuchsleistungszentrum) ta ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta VfL Wolfsburg.
Sana'ar Kasa
[gyara sashe | gyara masomin]A ranar 17 ga watan Mayu a shekarar 2016, an saka sunan Brandt a cikin tawagar farko na mutum 27 na Jamus don zuwa gasar cin kofin ƙasashen turai Yuro 2016. Ya kasance cikin 'yan wasan da za su taka leda a gasar Olympics ta bazara ta 2016, inda Jamus ta lashe lambar azurfa.
A ranar 4 ga Yuni 2018, an haɗa Brandt cikin tawagar mutane 23 na ƙarshe na Jamus don gasar cin kofin duniya ta FIFA na 2018.A ranar 17 ga watan Yuni, Brandt ya fara fitowa gasar cin kofin duniya a matsayin wanda zai maye gurbin Timo Werner a minti na 86 a wasan farko da Mexico inda suka sha kashi da ci 1-0.