Kader Mangane

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Kader Mangane
Rayuwa
Haihuwa Thiès (en) Fassara, 23 ga Maris, 1983 (41 shekaru)
ƙasa Faransa
Senegal
Karatu
Harsuna Faransanci
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
Union sportive du Rail (en) Fassara2000-2001174
  Neuchâtel Xamax (en) Fassara2001-200715014
  Senegal national association football team (en) Fassara2003-
R.C. Lens (en) Fassara2007-2008235
  BSC Young Boys (en) Fassara2007-200771
  BSC Young Boys (en) Fassara2007-200871
  Stade Rennais F.C. (en) Fassara2008-20121029
  Al Hilal SFC2012-2015142
Kayseri Erciyesspor (en) Fassara2013-2014272
Sunderland A.F.C. (en) Fassara2013-201320
Kayseri Erciyesspor (en) Fassara2014-2015
Gazélec Ajaccio (en) Fassara2015-
 
Muƙami ko ƙwarewa centre-back (en) Fassara
Lamban wasa 15
Tsayi 193 cm

Abdou Kader Mangane (an haife shi ranar 23 ga watan Maris ɗin shekara ta 1983) tsohon ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne kuma ɗan ƙasar Senegal wanda ya taka leda a matsayin mai tsaron gida. Ya shafe yawancin aikinsa a Faransa. A matakin ƙasa da ƙasa, ya buga wa tawagar ƙasar Senegal wasanni 23 inda ya ci ƙwallo 1.[1]

Aikin kulob[gyara sashe | gyara masomin]

Mangane ya fara aikinsa a ƙasarsa ta Senegal kafin ya koma Switzerland da Neuchâtel Xamax a cikin shekarar, 2001, inda kuma ya shafe shekaru shida. Sannan ya tafi buga wasanni biyar a Ligue 1 na Faransa, don Lens[2] a lokacin kakar shekara ta, 2007 zuwa 2008, da Rennes.[3]

A ranar 17 ga watan Yulin shekara ta, 2012, Mangane ya rattaɓa hannu kan kwangilar shekaru uku tare da kulob ɗin Al-Hilal na Saudiyya kan kuɗin da ba a bayyana ba.[4]

Ya koma ƙungiyar Sunderland ta Premier League a matsayin aro har zuwa ƙarshen kakar wasa a ranar 14 ga watan Janairun shekara ta, 2013.[5]

A ranar 31 ga watan Yulin shekara ta, 2015, Mangane ya rattaɓa hannu kan Gazélec Ajaccio akan kwangilar shekara guda.[6]

Rigima[gyara sashe | gyara masomin]

A ranar 21 ga watan Maris a shekara ta, 2009, yayin wasan Ligue 1 da Valenciennes ya yi wa ɗan wasan gaba Jonathan Lacourt rauni sosai a wani ƙalubale wanda ya haifar da karaya biyu na tibia da fibula. An dakatar da shi har zuwa ranar 1 ga watan Yunin shekara ta, 2009.[7]

Rayuwa ta sirri[gyara sashe | gyara masomin]

Mangane ya sami takardar zama ɗan ƙasar Faransa a ranar 16 ga watan Mayun shekara ta, 2011.[8]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

Hanyoyin haɗi na waje[gyara sashe | gyara masomin]