Kaltouma Nadjina (an haife ta a watan Nuwamba ranar 16, shekarar 1976) 'yar ƙasar Chadi ce mai wasan tsere. Ta ƙware a tseren gudun fanfalaƙi mai tazarar mita 200 da 400, kuma ta ajiye tarihi a jerin tseren gudun mita 100, da kuma mita 800 a ƙasar Chadi. Ta lashe gasar gudun fanfalaƙi na tsayin mita 200 a shekarar 2001 Jeux de la Francophonie da aka gudanar a Ottawa, Ontario, Canada da kuma wani mai tazarar mita 200 da mai mita 400 a gasar gudun fanfalaƙi na Afirka a shekarar 2002 da aka gudanar a Tunis.
An haife ta a Bol ga dangi na gari, aikin wasanta ya fara ne lokacin da ta halarci Makon Wasannin Ƙasa na shekarar 1993 a Moundou zuwa Makon Wasannin Kasa. Nasarar da ta yi a tseren mita 400 ya bude mata hanyar zuwa matakin da aka zaɓe ta a gasar cin kofin duniya ta matasa na shekarata 1994 da aka gudanar a Lisbon .