Kamfanin Black House Media

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Kamfanin Black House Media
URL (en) Fassara http://bhmng.com
Iri yanar gizo
Service entry (en) Fassara 2006

Black House Media (BHM) hukuma ce ta hulda da jama'a da sadarwar na zamanii da ke da hedikwata a Legas tare da ofis a London, United Kingdom. Adekunle Ayeni ne ya kafa ta a cikin shekara ta 2006, kamfanin yana kula da shirye-shiryen sadarwa na dabarun don kamfanoni masu sha'awar nishaɗi, salon rayuwa da kwalliya, kafofin watsa labaru, mabukaci da fasaha.

Asali[gyara sashe | gyara masomin]

Gidan Watsa Labarai na Black House ya soma ne daga gidan nisashi na All You Ever Need in Entertainment (AYENI Entertainment), kamfanin hulda na jama'a, wanda a yanzu ya shude. Bayan mai kamfanin Adekunle Ayeni ya sake suna ga tashar AYENI Entertainment, BHM ta fara aiki inda ta dauki Fagbule Olanike a matsayin ma’aikaci na farko. Kamfanin yana ɗaukar ƙa'idodi da ayyuka na al'ada, zamantakewa da hulɗar jama'a na dijital. Ayeni ya ruwaito cewa kamfanin ya zarce darajar dala miliyan daya a 2012, kuma yana da "kusan ma'aikata 60" a matsayin ma'aikata. A cikin shekara ta 2013, kamfanin ya zama memba na Ƙungiyar Masu Ba da Shawarar Jama'a ta Najeriya (PRCAN), ƙungiya ce ta kasuwanci da aka kafa a 1984 don masana'antar hulda da jama'a a Najeriya.

Kungiyar ‘Yan Jarida ta Najeriya, a wani rahoto da ta fitar kan harkar hulda da jama’a a Najeriya, ta bayyana BHM a matsayin daya daga cikin gidajen huldar jama'a guda 8 daga cikin 48 wanda ke biyan ma'aikansu akan lokaci. Raheem Akingbolu na This Day, a cikin rahotonsa mai suna "Shekaru 54 Bayan, Sashin Kasuwancin Har yanzu yana fuskantar ƙalubale masu yawa", ya bayyana kamfanin a matsayin "jagora a fannin huldar jama'a na zamani". A Najeriya, an kuma bayyana BHM a matsayin "kamfanin hulda da jama'a wanda ake kyautata zaton cewa kamfanin na gudanar da mafi yawan harkokin nishadi."

Aikace-aikacen BHM[gyara sashe | gyara masomin]

A cikin shekara ta 2012 ne , Black House Media ta haɓaka ƙungiya ta masana software da masu haɓaka BHM App, "app na wayar hannu na farko na huldar jama'a" kuma "yunkuri na farko." App din na daga cikin tarin ayyuka ne na ma'aikatan hulda da jama'a na Najeriya, wanda aka tsara don biyan buƙatun masu amfani da app a Najeriya.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

Hanyoyin haɗi na waje[gyara sashe | gyara masomin]