Kande Balarabe
Kande Balarabe | |||
---|---|---|---|
| |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Saliyo, | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Karatu | |||
Harsuna | Turanci | ||
Sana'a | |||
Sana'a | gwagwarmaya da ɗan siyasa |
Sa'adatu Kande Balarabe 'yar siyasan Najeriya ce daga jihar Kano. Tana cikin mata uku da aka zaba a Majalisar Wakilan Najeriya a shekarar 1983. Ta yi aiki a wurare daban-daban a cikin jiharta ciki har da daraktar hukumar mata ta jihar Kano.
Rayuwa
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Balarabe a Saliyo inda mahaifinta ke kasuwanci. Ta halarci makarantar mata ta Freetown da Royal School for Nursing a London. A 1982, a lokacin Jamhuriya ta biyu, Kande ta zama shugabar mata reshen mata na PRP a Kano. Kafin ta shiga siyasa, ta kasance ma’aikaciyar jinya a asibitin jihar, [1] mai suna asibitin Murtala Mohammed da ke Kano. Koyaya, a 1982, ta yi murabus don ta kashe mafi yawan lokacinta a siyasa. A cikin 1983, ta yi takara kuma ta sami kujera a Majalisar Wakilan Najeriya, amma, an yanke jamhuriya ta biyu. A shekarar 1987, ta zama mamba a majalisar wakilai, tana wakiltar wata gunduma a cikin jiharta sannan daga baya aka nada ta Darakta a Hukumar Mata ta Jihar Kano.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Nelson, B. J., & Chowdhury, N. (1994). Women and politics worldwide. New Haven: Yale Univ. Press. P. 516