Kanta Museum

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Kanta Museum
Hukumar Kula da Gidajen Tarihi ta Kasa
ethnographic museum
Wuri
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya
JihaKebbi
Ƙaramar hukuma a NijeriyaArgungu
Coordinates 12°44′58″N 4°32′12″E / 12.7495°N 4.5367°E / 12.7495; 4.5367
Map
History and use
Opening1958
Manager (en) Fassara Hukumar Kula da Gidajen Tarihi ta Kasa Hukumar Kula da Gidajen Tarihi ta Kasa
Contact
Address PGXP+QMF, 861101, Argungu da Kanta Museum, P.M.B. 1001 Argungu, Kebbi State.
Offical website

Kanta Museum wani gidan kayan gargajiya ne a Argungu, Najeriya, kusa da babbar kasuwa. An gina ginin a shekarar 1831, an sa wa ginin sunan Muhammed Kanta, wanda ya kafa Masarautar Kebbi a shekarar 1515. Yakubu Nabame, tsohon Sarkin Kebbi ne ya gina shi, kuma ya kasance fadar sarki har zuwa 1942 lokacin da turawan Ingila suka gina sabuwar fadar mulki a zamanin Muhammad Sani . Bayan ginin ya zama babu kowa, a ranar 1 ga Yuli, 1958, ya buɗe a matsayin gidan tarihi, yana ba da haske game da rikice-rikicen tarihin jihar Kebbi . Gidan kayan tarihi ya kasu kashi goma sha daya kuma yana da tarin makamai masu ban mamaki, wadanda suka hada da laya, mashi, takuba, itace, duwatsu, baka da kibau, bindigogin gida har ma da ganguna da ake nunawa.[1]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Next Archived 2011-07-21 at the Wayback Machine