Jump to content

Kasar Katar a Idon Matafiya (Littafi)

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Kasar Katar a Idon Matafiya (A Larabce: قطر في عيون الرحالة) littafi ne wanda Ali bn Ghanim Alhajiri, babba kuma haziƙin marubucin nan ɗan kasar Ƙatar, ya wallafa kan tarihin kasar Katar tun zamanin da ya shude kafin maladiya har ya zuwa bayan zuwan musulunci. Manyan masu fassara sun fassara littafin zuwa yarika ciki harda Sinanci da Sipaniyanci. A nan baya bada dadewa ba fassara hausa da Yarbanci na wannan littafi ya fito.[1]

Kunshiya[gyara sashe | gyara masomin]

Wannan littafi yana ɗauke ne da babi huɗu a cikinsa, inda babi na farko yake tattaunawa a game da ma’anar sunan Qatar a cikin harshen Larabci, tare kuma da yin ƙarin bayani a kan  dangantakar sunan Ƙatar da rayuwar mutanen yankin. Kamar kuma yadda ya yi bayani dalla-dalla a game da yadda sunan Ƙatar ya zo a cikin littattafan tarihi da na matafiya.

Babi na biyu kuwa ya yi tsokaci ne a game da matakan tarihi masu muhimmanci na ƙasar Ƙatar a cikin Zamanunnuka daban-daban da suka gabata, wanda ya ƙunshi dangantakar Ƙatar da ƙasar Iraki da garuruwan Sham da Bahrain da Uman da Hijaz da kuma Misra, kamar kuma yadda ya ƙunshi alaƙoƙin Qatar da wasu al’ummomi tun shekaru dubu biyar kafin Miladiya. Hakanan kuma wannan babi ya yi tsokaci a game da alaƙoƙin Ƙatar da ƙasashe da dama bayan Miladiyya, sannan kuma ya yi bayani akan matakan tarihi masu muhimmanci na Ƙatar a lokacin musulunci tun daga bayyanar hasken musulunci har ya zuwa zamanin Umayyawa da kuma Abbasiyyawa.

Babi na uku kuwa ya yi ƙarin bayani ne agame da yanayin tattalin arzikin Ƙatar tun a can baya, wanda hakan ya ƙunshi abubuwan da ƙasar ta shahara da su na noma da kiwo da kasuwanci da sana’oi iri-iri, waɗanda suka haɗa da sana’ar hannu, kamar saƙa da na ƙera makamai da sana’ar gina Tukwane da Tandodi da kayayyakin Sana’a, waɗanda suka haɗa da ɗanyun albarkatu da ma’aikata, dakuma dai sauran sanao’I daban-daban.

Amma kuwa babi na huɗu ya yi tsokaci ne akan tarihin hanyoyin kasuwanci na ƙasar Ƙatar, waɗanda suka haɗa da shaharar Qatar ta ɓangaren dakarun ruwa, da tashoshin jiragen ruwa da jiragen ruwa da kuma Ilimin Qatar ta ɓangaren sanin kimiyyar ruwa. Hakanan kuma hanyoyin kasuwancin na kan ruwa da na ƙasa.[2]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. https://www.alukah.net/culture/0/156766/%D9%82%D8%B1%D8%A7%D8%A1%D8%A9-%D9%81%D9%8A-%D9%83%D8%AA%D8%A7%D8%A8-%22%D9%82%D8%B7%D8%B1-%D9%81%D9%8A-%D8%B9%D9%8A%D9%88%D9%86-%D8%A7%D9%84%D8%B1%D8%AD%D8%A7%D9%84%D8%A9%22-%D9%84%D9%84%D8%AF%D9%83%D8%AA%D9%88%D8%B1-%D8%B9%D9%84%D9%8A-%D8%A8%D9%86-%D8%BA%D8%A7%D9%86%D9%85-%D8%A7%D9%84%D9%87%D8%A7%D8%AC%D8%B1%D9%8A/
  2. https://msheirebmuseums.com/ar/product/%D9%82%D8%B7%D8%B1-%D9%81%D9%8A-%D8%B9%D9%8A%D9%88%D9%86-%D8%A7%D9%84%D8%B1%D8%AD%D8%A7%D9%84%D8%A9/