Kasko

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Kasko
Bayanai
Ƙaramin ɓangare na tableware (en) Fassara da akwati

Kasko jam'in kasko shine kasake, kasko wani abu ne da ake amfani da shi a gida don turara hayaƙi na magani ko kuma turare irin na wuta, da dai sauransu. Kasko kala-kala ne akwai babba akwai ƙarami, yanzu da aka samu cigaba hadda mai penti (paint), akwai kuma baƙin kasko wanda muka gada iyaye da kakanni. Ana gina kasko ne da yanɓu na ƙasa kamar yadda ake gina tukunyan ƙasa. Akwai karin magana da hausawa keyi "mutuwar kasko"[1] ma'ana duk an taru an rasa wato cikin ɗayan abu biyu ƙila duka an rasa su. Haka kuma wajen dambe ana yin mutuwar kasko.

Kasko me penti

Baƙin kasko

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Usman, Jamil (23 June 2020). "Mutuwar kasko: Miji ya soka wa matarsa wuka sannan ya sha guba". Hausa.legit.ng. Retrieved 31 October 2021.