Kasuwar Bello

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Kasuwar Bello

Kasuwar Bello, kasuwa ce a Yanar gizo ta farko dake amfani da harshen Hausa. Wani matashi dan Najeriya ne mai suna Bello Galadanci, wanda ya yi fice a harkar koyar da hanyoyin ci gaban kasuwanci ga matasa a yanar gizo, kuma mai burin ganin cigaban matasa ya yi nasarar bude sabuwar Kasuwar Hausa ta farko a yanar gizo wanda ke ko'ina a duk fadin duniya. [1] a halin yanzu kasuwar Bello Nada reshunan ta a wasu yankunan kasashen Afirka ta yamma, kuma tana da shelkwatarta ne a kasar Sin. Kasuwar Bello tana tattara ‘yan kasuwa da sana’o’i a waje daya domin su samu kudi, tare da basu sababbin dabarun zamani na kasuwanci da gina tattalin arziki. Kasuwar Bello na baiwa ‘yan kasuwa hanyoyin samun bayanai akan ko wani irin kaya dake kasashen Duniya musamman Sin da Amurka da ma shiri na musamman domin sayo musu da aika musu har gida a Najeriya da Nijar. Kasuwar Bello na baiwa kamfanoni shawarwarin hanyoyin bunkasa harkokinsu da fitar da kaya zuwa kasashen waje. Kasuwar Bello na da shiri na musamman na nemar wa dalibai makarantu da ma baiwa matasa tallafin karatu zuwa kasashe daban-daban a duk fadin duniya. Kasuwar Bello na koyawa kananan ‘yan kasuwa hanyoyi masu sauki na tallata sana’o’in su akan yanar gizo da neman cigaba. Kasuwar Bello na koyar da harsunan kasashen waje ga duk wanda yake sha’awar tafiya kasuwanci. Kasuwar Bello na bada shagunan yanar gizo kyauta ga duk wanda yake bukata da koya masa yadda ake samun kudi da su[2]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2018-03-19. Retrieved 2018-03-17.
  2. www.kasuwarbello.com