Kasuwar Dawanau

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Kasuwar Dawanau
kasuwa
Bayanai
Ƙasa Najeriya
Wuri
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya
Jihajihar Kano

Kasuwar Dawanau Ita ce kasuwar hatsi mafi girma a Nahiyar Afirka, saboda da girma na hada-hadar kasuwanci da ya ke faruwa a cikin kasuwar a kullum.Tana cikin garin Dawanau dake Karamar Hukumar Dawakin Tofa a jihar Kano, Najeriya.

Tarihi[gyara sashe | gyara masomin]

Kasuwar Dawanau tsohuwar kasuwar hatsi ce a Najeriya da Afirka.Tana cikin garin Dawanau, Ƙaramar Hukumar Dawakin Tofa a jihar Kano.

Ayyuka[gyara sashe | gyara masomin]

Kasuwar Dawanau ta kasance kasuwar hatsi mafi girma a Afirka. Tana tattara masu saye da sayarwa daga ƙasashe daban-daban na Afirka, Turai, Asiya, Amurka da Saudia. Ana kuma safarar kayayyaki a kowace rana zuwa Togo, Burkina Faso, Kamaru, Chadi, Nijar, Ghana tsakiyar Afirka, Afirka ta Kudu, libya da sauran ƙasashen Afirka. A wajen Afirka, yan kasuwa daga Burma, Dubai, India, China, Burtaniya, Saudi Arabia, America da sauran ƙasashe suma suna tallafawa kasuwar hatsi don abubuwa kamar su zogale da ganyaye, iri essame, furen Hibuscus (Sobu) da sauran abubuwa kamar suya wake, Wake, Rogo, Gero, masarar Guinea, da sauran abubuwa. [1]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. https://allafrica.com/stories/201604110924.html

.