Jump to content

Kasuwar Dawanau

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Kasuwar Dawanau
kasuwa
Bayanai
Ƙasa Najeriya
Wuri
Map
 12°05′11″N 8°26′29″E / 12.086286°N 8.441254°E / 12.086286; 8.441254
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya
Jihohin Najeriyajihar Kano
kasuwar dawanau

Kasuwar Dawanau Ita ce kasuwar hatsi mafi girma a Nahiyar Afirka, saboda da girma na hada-hadar kasuwanci da ya ke faruwa a cikin kasuwar a kullum.Tana cikin garin Dawanau dake Karamar Hukumar Dawakin Tofa a jihar Kano, Najeriya.

Kasuwar Dawanau tsohuwar kasuwar hatsi ce a Najeriya da Afirka.Tana cikin garin Dawanau, karamar Hukumar Dawakin Tofa a jihar Kano.

Kasuwar Dawanau ta kasance kasuwar hatsi mafi girma a Afirka. Tana tattara masu saye da sayarwa daga kasashe daban-daban na Afirka, Turai, Asiya, Amurka da Saudia. Ana kuma safarar kayayyaki a kowace rana zuwa Togo, Burkina Faso, Kamaru, Chadi, Nijar, Ghana tsakiyar Afirka, Afirka ta Kudu, libya da sauran kasashen Afirka. A wajen Afirka, yan kasuwa daga Burma, Dubai, India, China, Burtaniya, Saudi Arabia, America da sauran kasashe suma suna tallafawa kasuwar hatsi don abubuwa kamar su zogale da ganyaye, iri essame, furen Hibuscus (Sobu) da sauran abubuwa kamar suya wake, Wake, Rogo, Gero, masarar Guinea, da sauran abubuwa. [1]

  1. https://allafrica.com/stories/201604110924.html

.