Kasuwar Doya ta Yaki Biam
Kasuwar Doya ta Yaki Biam |
---|
Kasuwar doya ta Zaki Biam ita ce kasuwar doya mafi girma a faɗin duniya. Kasuwa ce ta kowa da kowa da ke garin Zaki Biam, wani gari a Ƙaramar hukumar Ukum a jihar Benue, Najeriya. Kasuwar ta shahara wajen sayar da doya, wadda doya itace babbar amfanin gona da ake nomawa a yankin. Ita ce babbar cibiyar kasuwancin doya, da ke jawo hankalin masu saye da sayarwa daga sassa daban-daban na Najeriya da makwaftan ƙasashe.
Kasuwar Zaki Biam ita ce babbar kasuwar da ake saida kaya kala ɗaya wato doya (Mono-product) a Najeriya.[1][2]
Kasuwar tana jan hankalin masu saye da sayarwa daga yankuna daban-daban na Najeriya da ma kasashen makwabta. Manyan ƴan'kasuwa daga ƙasashe irin su Kamaru, Nijar da Ghana sune suke sayen doya a kasuwar.[2] Kimanin manyan tireloli ɗari biyu (200) na doya ne ke tashi daga kasuwar a kullum, kuma duk da haka doyar bata ƙarewa.[3][4]
A watan Yunin 2020 ne gwamnatin tarayyar Najeriya ta ƙaddamar da wani wurin ajiyar kaya a kasuwa domin zama cibiyar hada-hada ga jihohin da ke da albarkatun noma na doya kamar Nasarawa, Taraba Neja da ita kanta jihar Benuwai ɗin. Sake gina kasuwar wanda ya ƙunshi rumfuna 660 da aka sake ginawa, tituna na cikin gida, gine-ginen gudanarwa da kuma rijiyar burtsatse mai amfani da hasken rana.[5]
Najeriya ce kan gaba wajen samar da doya, inda take alfahari da yawan tan miliyan 17 a duk shekara, wanda ya zama kaso 70-76% na abin da ake nomawa a duniya. Galibin wannan doyar l, wadda adadinta ya kai kusan miliyan biyu a mako, suna bi ta Kasuwar Zaki Biam, wanda ke nuni da wata babbar cibiya a hanyar rarraba kayayyakin gona na doya.[6]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Ugbede, Lois. "Does Nigeria have the biggest Yam market in the World?". dubawa.org. Centre For Journalism Innovation & Development. Retrieved 27 June 2023.
- ↑ 2.0 2.1 "Zaki Biam Yam Market Benue State". connectnigeria.com. Retrieved 27 June 2023.
- ↑ "The Sorry Story Of Zaki-Biam Yam Market". dailytrust.com. Retrieved 20 December 2023.
- ↑ "The World's Biggest Yam Market Located in Benue, Nigeria; Zaki Biam International Yam Market". newscentral.africa. Retrieved 20 December 2023.
- ↑ "MSMEClinic gets 200,000 capacity yam storage facility in Benue". nairametrics.com. Retrieved 20 December 2023.
- ↑ "Top 100 famous markets in the world – P85 - Zaki Biam market (Nigeria): Busiest yam market in Africa". worldkings.org. Retrieved 20 December 2023.