Jump to content

Kathleen Okafor

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Kathleen Okafor
Rayuwa
Sana'a
Sana'a Malami

Kathleen Ebelechukwu Okafor farfesa ce ta Najeriya a fannin shari'ar dukiya da kasuwanci (Property and commercial law) kuma mukaddashiyar shugaban jami'ar Baze.[1][2]

Rayuwar farko da asali

[gyara sashe | gyara masomin]

Kathleen ta samu jarrabawar O'Level a Queens School Enugu kuma ta samu LL. B a Jami'ar Nigeria, Nsukka a shekara ta 1974. Daga nan ta wuce makarantar koyon aikin lauya ta Najeriya a Legas kuma aka kira ta zuwa Bar a shekarar 1979. An daukaka ta zuwa matsayin Babbar Lauyar Najeriya a watan Satumba 2022 ta Lauyoyin Najeriya.[3][4]

Ta samu LL. M digiri daga Jami'ar College London a shekara ta 1981 da kuma PhD daga Jami'ar Legas a shekara ta 2000.[5][6]

Kathleen Okafor ta yi aiki a takaice a cikin Lateef Adegbite & Co Chambers. Ta kasance mai ba da shawara ta biyu tare da Shell Petroleum daga can ta ci gaba da aiki a matsayin mai ba da shawara kan harkokin shari'a kuma sakatariyar kamfani na Kamfanin wallafawa da Ma'adinan Tsaro na Najeriya (Nigerian Security Printing and Minting Plc.).[7]

A wani bangare na ayyukanta na jagoranci, ta kasance Dean, Faculty of Law Baze University kuma shugabar kwamitin kula da harkokin shari'a.

Majalisar gudanarwa ta Jami’ar Baze ta naɗa ta a matsayin mukaddashiyar mataimakiyar shugaban jami’ar a watan Agusta 2023 bayan naɗin tsohon mataimakin shugaban jami’ar, Farfesa Tahir Mamman a matsayin ministar ilimi da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi.[8][9]

  1. "Baze University Abuja". bazeuniversity.edu.ng. Retrieved 2023-08-25.
  2. "Baze University Abuja". bazeuniversity.edu.ng. Retrieved 2023-08-25.
  3. Osasona, Kehinde (2022-09-30). "Nine Law Professors, 3 Lawyers, 50 others elavated to Senior Advocates of Nigeria". Blueprint Newspapers Limited (in Turanci). Retrieved 2023-08-25.
  4. Oyeyemi, Fadehan (2022-09-29). "9 professors, 3 EFCC lawyers, 50 others emerge Senior Advocates of Nigeria". Daily Post Nigeria (in Turanci). Retrieved 2023-08-25.
  5. "'There's Gender Inequality at the Inner Bar' - THISDAYLIVE". www.thisdaylive.com (in Turanci). Retrieved 2023-08-25.
  6. "About Us – Dr Kathleen Okafor Chambers" (in Turanci). Archived from the original on 2023-08-25. Retrieved 2023-08-25.
  7. "Restructuring and insolvency in Nigeria – Events". www.legal500.com. Retrieved 2023-08-25.
  8. gidado (2023-08-18). "Prof. Kathleen Okafor Appointed Acting VC of Baze University, Succeeding Prof. Tahir Mamman". News Digest (in Turanci). Retrieved 2023-08-25.
  9. "TAHIR MAMMAN: RIGHT MAN, RIGHT JOB - THISDAYLIVE". www.thisdaylive.com (in Turanci). Retrieved 2023-08-25.