Kau da Bautan Bayi
| |
Iri |
harkar zamantakewa political movement (en) |
---|---|
Nufi | abolition of slavery (en) |
Kawo karshen Bautan Bayi wato Abolitionism, ko kuma Kungiyar kau da bautan bayi, wani yunkuri ne don kawo karshen Bautar da bayi don kuma 'yantar da bayi a duniya.
Kasa ta farko da ta haramta bautar da bayi ita ce Faransa a cikin 1315, amma sai daga baya aka yi amfani da hakan kasashen da take mulka. A karkashin ayyukan Toyotomi Hideyoshi, an soke bautar da dangi a duk faɗin Japan tun 1590, kodayake an yi amfani da wasu nau'ikan aikin tilas a lokacin yakin duniya na biyu. Kasa ta farko kuma ita kadai da ta 'yantar da kanta daga bautawar ita ce tsohuwar mulkin mallaka na Faransa, Haiti, sakamakon Juyin Juya Halin 1791-1804. Yunkurin kawar da bautarwa na Burtaniya ya fara ne a ƙarshen karni na 18, kuma Shari'ar Somersett ta 1772 ta tabbatar da cewa bautar ba ta wanzu a cikin dokar Ingilishi. A cikin 1807, an haramta cinikin bayi a duk faɗin Daular Burtaniya, kodayake ba a 'yantar da bayi da ke cikin mulkin mallaka na Burtaniya ba har sai Dokar kawar da bautar a cikin 1833. Vermont ita ce jiha ta farko a Amurka da ta soke bautar a shekara ta 1777. A shekara ta 1804, sauran jihohin arewa sun soke bautar amma ta kasance doka a jihohin kudanci. A shekara ta 1808, Amurka ta haramta shigo da bayi amma ba ta haramta bautar ba - sai dai a matsayin horo - har zuwa 1865.