Kisan gilla a Gamboru Ngala, 2014
| ||||
Iri | aukuwa | |||
---|---|---|---|---|
Kwanan watan | 5 Mayu 2014 | |||
Wuri | Gamboru | |||
A daren ranar 5-6 ga watan Mayun 2014, mayaƙan ƙungiyar Boko Haram sun kai hari a tagwayen garuruwan Gamboru da Ngala a jihar Borno, arewa maso gabashin Najeriya.[1] Kimanin mazauna garin 310 ne aka kashe a kisan a harin na tsawon sa’o’i 12, kuma an lalata garin sosai.[2][3][1]
A cikin wannan dare ne Boko Haram suka sace ƴan mata takwas masu shekaru tsakanin 12-15 daga arewa maso gabashin Najeriya,[4][5] daga baya adaɗin ya kai goma sha ɗaya.[6]
Bayan fage
[gyara sashe | gyara masomin]Akwai Gamboru jami’an tsaro a sansanin Ngala da suka bar garin kafin a kai harin domin bibiyar waɗanda suka yi garkuwa da ‘yan matan makarantar Chibok.[7]
Ana kallon jihar Borno a matsayin babbar cibiyar Boko Haram.[7] A cewar Sanatan Najeriya Ahmed Zanna da wasu mazauna garin, jami'an tsaron sun bar Gamboru Ngala ne bayan da mayakan Boko Haram suka yaɗa jita-jita cewa an ga ƴan matan makarantar da aka yi garkuwa da su.[8]
Kisa
[gyara sashe | gyara masomin]Ƴan ta’addar ɗauke da bindigogi kirar AK-47 da RPG, sun kai hari a garin kan wasu motoci sulke guda biyu da suka sace daga hannun sojojin Najeriya watanni da dama da suka gabata.[9] Ƴan ta’addan sun buɗe wuta kan mutanen a wata kasuwa mai cike da cunkoson jama’a da ake buɗewa da daddare lokacin da yanayin zafi ya kwanta.[10] Bayan ƙona gidaje, mayakan sun bindige mutanen da suka yi ƙoƙarin tserewa daga gobarar.[2]
An fara gano adadin waɗanda suka mutu a hukumance su 200 a ranar 7 ga watan Mayu. Zanna da Waziri Hassan wasu mazaunin yankin duk sun ba da rahoton mutuwar aƙalla mutane 336.[9]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ 1.0 1.1 de Montclos, Marc-Antoine Pérouse (2017-05-08), "Boko Haram", Understanding Boko Haram, Routledge, pp. 19–40, doi:10.4324/9781315525051-2, ISBN 978-1-315-52505-1, retrieved 2020-05-16
- ↑ 2.0 2.1 "Boko Haram Attack Kills Hundreds In Border Town". The Huffington Post. Retrieved 7 May 2014.
- ↑ "Terrorism survivor in Cameroon takes road to recovery: UN News special report". UN News (in Turanci). 2019-08-19. Retrieved 2020-02-05.
- ↑ "Boko Haram kidnaps more girls in Nigeria", ABC, AU, 6 May 2014
- ↑ Suspected Boko Haram gunmen kidnap eight girls from village in Nigeria. Monica Mark, The Guardian website; Tuesday 6 May 2014 19.21 BST.
- ↑ Boko Haram kidnaps more children, kills villagers in Nigeria. Sabrina Ford, Laura Italiano and Post Wires; New York Post, May 11, 2014 | 1:35am.
- ↑ 7.0 7.1 Жертвами нападения "Боко Харам" на город в Нигерии стали 300 человек (in Russian). RIA Novosti. Retrieved 7 May 2014.CS1 maint: unrecognized language (link)
- ↑ "Nigeria confirms market massacre blamed on Boko Haram". BBC. Retrieved 10 May 2014.
- ↑ 9.0 9.1 Adam Nossiter. "Islamist Militants Kill Hundreds of Civilians in Northeastern Nigeria". The New York Times. Retrieved 10 May 2014.
- ↑ "Nigerian official: Hundreds killed in attack". The Washington Post. Archived from the original on 8 May 2014. Retrieved 7 May 2014.