Kisan kiyashi a Damboa
Appearance
| ||||
| Iri | Kisan Kiyashi | |||
|---|---|---|---|---|
| Kwanan watan |
4 ga Yuli, 2014 18 ga Yuli, 2014 | |||
| Wuri | Jihar Borno | |||
A ranar 4 ga watan Yulin 2014 ne ƙungiyar Boko Haram ta kai hari garin Damboa da ke jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya.[1] Rundunar sojin Najeriya ta ce sun fatattaki ƴan ta’addan, amma mazauna yankin sun ce sojojin sun yi watsi da barikinsu na can suka bar garin a dalilin haka. [1]
A ranar 18 ga Yuli, 2014, Boko Haram sun sake kai hari a garin Damboa ɗin.[2] Sojojin sun tafi; ‘Yan Boko Haram sun yi nasarar fatattakar ‘yan sa kai cikin gaggawa, inda suka kwace garin – kuma suka kashe sama da mutane 100 tare da ƙona mafi yawan mutane da suka kashe. [2]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- 1 2 "Boko Haram insurgents kill 100 people as they take control of Nigerian town". The Guardian. 2014-07-19. Archived from the original on 2022-11-09.
- 1 2 "Nigeria: Boko Haram tue au moins 100 personnes". lapresse.ca. Retrieved 2020-04-11.
