Yakin Damboa
Iri |
rikici faɗa |
---|---|
Bangare na | Rikicin Boko Haram |
Kwanan watan | 6 Oktoba 2013 |
Wuri | Damboa |
Ƙasa | Najeriya |
Yaƙin Domboa an yi shi ne tsakanin rundunar soja ta 7 ta Najeriya da masu tayar da ƙayar baya na Boko Haram da safe a ranar 6 ga Oktoba 2013.[1] Boko Haram ta shiga ƙauyen da ƙarfe 4:30 na safe, sun tilasta limami na masallacin yankin ya yi kira ga fararen hula su zo masallacin bayan haka suka buɗe musu wuta, suka kashe bakwai kuma suka ji wa mutane da yawa rauni.[2] Masu tayar da ƙayar baya sun sami nasarar ƙone gine-gine da yawa kafin sojojin Najeriya su shiga tsakani, bayan haka rikice-rikicen da suka faru inda aka kashe masu tayar da hankali na Boko Haram 15, wasu masu tayarwar sun tsere. Sojojin Najeriya sun ƙwace bututun grenade guda dayya, bama-bamai biyu na gurneti, bindigogi biyar na AK 47, motar karɓa da kuma harsashi iri-iri daga masu tayar da kayar baya.[1]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ 1.0 1.1 "20 killed Nigeria terrorist attack". DNA India (in Turanci). 2013-10-06. Retrieved 2021-01-15.
- ↑ "Nigerija: Sedam ubijenih u džamiji". RTCG - Radio Televizija Crne Gore - Nacionalni javni servis (in Montenegrin). Retrieved 2021-01-15.