Kisan kiyashin Gubio

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Infotaula d'esdevenimentKisan kiyashin Gubio
Map
 12°29′46″N 12°46′44″E / 12.496°N 12.779°E / 12.496; 12.779
Iri Kisan Kiyashi
Kwanan watan 9 ga Yuni, 2020
Wuri Gubio
Jihar Borno
Wanda ya rutsa da su bakwai
Adadin waɗanda suka rasu 82
Adadin waɗanda suka samu raunuka 13
Perpetrator (en) Fassara Boko Haram
Has part(s) (en) Fassara
Q96283949 Fassara

Da yammacin ranar 9 ga watan Yuni, shekarar 2020, an yi wani kisan gilla a wani ƙauye da ke karamar hukumar Gubio a jihar Borno, arewa maso gabashin Najeriya. [1] [2] [3] Wasu gungun ‘yan bindiga kan babura da wasu motoci sun kai farmaki a ƙauyen na sama da sa’o’i biyu, inda suka kashe akalla mutane 81.[1] [2] [3][4] An jikkata wasu mutane 13 a harin, yayin da wasu bakwai suka yi awon gaba da su. [4] Maharan sun kuma kashe shanu sama da 300 tare da sace wasu 1,000. [2] [3] Wani jirgin yakin sojin sama ya yi luguden wuta kan maharan a lokacin da suke tafiya. [2] Washe gari ne maharan suka dawo inda suka kashe wani makiyayi da ya tsallake rijiya da baya, sannan suka kona kauyen. [1] [2] Babu wata kungiya da ta ɗauki alhakin kai harin, amma ana zargin kungiyar Boko Haram mai da'awar jihadi . [1] [2]

A ranar ne wasu ’yan daba su 200 suka kai hari a ƙauyen Kadisau da ke Jihar Katsina. [1] Sun yi awon gaba da wasu, inda suka kashe akalla mutane 20 da suka yi kokarin kare garin. [1] Hakazalika Babu wata kungiya da ta ɗauki alhakin hakan. [1]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. 1.0 1.1 1.2 1.3 1.4 1.5 1.6 Fighters kill dozens, raze village in Nigeria's Borno State
  2. 2.0 2.1 2.2 2.3 2.4 2.5 Suspected Boko Haram fighters kill 69 in Nigeria's northeast
  3. 3.0 3.1 3.2 Boko Haram militants leave 70 dead in northeast Nigeria attack
  4. 4.0 4.1 "Boko Haram kills 81, abduct seven in Borno attack". June 10, 2020 – via thenationonlineng.net.