Kitso

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search

Kitso wata al'ada ce da ake yin ta domin tufke gashin kai, saboda ado ko kwalliya ko kuma dalili na addini. A wasu ƙasashen akasari mata suka fi yin kitso yayin da a wasu ƙasashen maza kaɗai sukafi yin sa. A wasu kuma maza da mata ne ke yin kitso. Mata na kiste gashin kan su don kwalliya/Ado da birge mazajensu na Aure kitso yanada matuƙar muhimmanci sosai musamman ga wasu ƙabilun Afrika.[1]

Wasu matan ma sukan ɗauki kitso a matsayin sana'ar su ta yau da kullum kuma suna samun amfani. Kitso kala-kala ne akwai, akwai gargajiya da na zamani.[2]

Asalin Kitso[gyara sashe | Gyara masomin]

A tarihi idan muka koma shekaru 30,000 baya duk ya fara ne a Afirka. A hakikanin gaskiya, tsohon sanannen hoton kitso na kwalliya an gano shi a bakin Kogin Nilu, ta wani wurin da aka binne shi da ake kira Saqqara. Har ila yau an gano hoton kitso a jikin Giza. Kabilu, ƙungiyoyi da yankuna na Afirka sun kawata kawunan su saboda mahimmancin al'adu kuma sun kasance masu rikitarwa da banbanci kamar yawancin salon da muka sani kuma muke son sakewa a yau.

Yawa kamar salo a cikin tarihi, gashi ya daɗe da zama alama ta halayen mutum kamar matsayi na zamantakewar jama'a, dukiya, addini, shekaru, matsayin aure da sauransu.

Ire ire-iren kitso na gargajiya[gyara sashe | Gyara masomin]

 • Ayaba da wuka,
 • Bayan hanu,
 • Cikin-hanu,
 • Cuku,
 • Doka,
 • Gaban hanu,
 • Gammo,
 • Gudun biri,
 • Hittobe,
 • Kalaba,
 • Kifa-kwando,
 • Kwado,
 • Lallabtu,
 • Leka-tukunya,
 • Mai maciji,
 • Mu-gamu-a-kotu,
 • Mu-gamu-a-tasha,
 • Tashin soja,
 • tuntu,
 • Zane.

Ire-iren kitson Hausawa na zamani[gyara sashe | Gyara masomin]

 • 2 steps,
 • 6-3-3-4,
 • 7-7,
 • Abuja connection,
 • Baby face,
 • Come down love,
 • Ghana weaven,
 • Hular tsigai,
 • Husband and wife,
 • Ibra style,
 • Kitson zare,
 • My husband heart. Da dai sauransu.

Manazarta[gyara sashe | Gyara masomin]