Jump to content

Konda Reddis

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Konda Reddis
konda reddis

Konda Reddis ko Hill Reddis kabila ce na dake zaune a jihar Andhra Pradesh dake cikin kasar Indiya tana kuma makwabtaka da jihohin Odisha, Tamil Nadu. [1]

Ba su da alaka da kabilar Hindu kuma da aka fi sani da sunan Reddy.[2] Suna zaune galibi a gundumar ko yankin Khammam, tare da karami a gundumomin,ko yankuna Alluri Sitharama Raju da Eluru.[3] Ba a lissafa Konda Reddis a matsayin kabilun a jihar Odisha duk da bukatar mutane. Mutanen Konda Reddis kan yi magana da yaren Telugu yayin mu'amala da wadanda ba 'yan kabilarsu ba.[4] Kididdigar shekarar 1991 na Indiya ta kidaya 432 Hill Reddis.[ana buƙatar hujja] .

Addinin gargajiya na Konda Reddis ba su yarda da cewa akwai kurwa acikin jikin dan adam ba.[5] Ko da yake, mutanen Reddis suna bauta wa matattu kakanninsu, tuddai, gumakan gida, kuma sun yarda da allolin Hindus.[ana buƙatar hujja]

  1. "List of notified Scheduled Tribes" (PDF). Census India. pp. 21–22. Archived from the original (PDF) on 7 November 2013. Retrieved 15 December 2013.
  2. "Tribes of India". publishing.cdlib.org (in Turanci). Retrieved 2018-05-25.
  3. The Mango Dance of the Konda Reddis, webindia123.com.
  4. "Konda Reddy community demands ST status". The Hindu. Retrieved 7 December 2017.
  5. "Adherents.com". www.adherents.com. Archived from the original on 10 October 2003. Retrieved 2018-05-25.CS1 maint: unfit url (link)

Kara karantawa

[gyara sashe | gyara masomin]