Koumbou Boly Barry

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Koumbou Boly Barry 'yar siyasar ƙasar Burkina Faso ce wacce ta zama ministar ilimi da karatu na Burkina Faso. Ita ce Wakiliyar Majalisar Ɗinkin Duniya na musamman kan hakkin ilimi tun a shekarar 2016.[1] Boly Barry ta sami digiri na uku a fannin tarihin tattalin arziki daga Jami'ar Cheikh Anta Diop da ke Dakar, Senegal.[1] Ita ce minista a majalisar ministocin Luc-Adolphe Tiao.[2]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. 1.0 1.1 "Koumbou Boly Barry". Office of the United Nations Human Rights Commissioner.
  2. "ICAO Council President receives Prime Minister of Burkina Faso". ALN News. 18 June 2014.