Jump to content

Kundin Tsatsuba

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.


Kundin Tsatuba

Kundin tsatsabu littafi ne na yaƙi wanda ya shahara a lokacin da ludayinsa ke kan dawo. Kuma har zuwa yanzu kwarjini da riƙewar littafin a zuciyar masu karatu tana nan. Labarin ya zagaye ya karaɗe sassa daban-daban saboda farin jinin da yake da shi. Marubucin ya taka rawar gani matuƙa wurin sarrafa alaƙalaminsa tare da samar da labari mai tsayi tare da armashi.[1]

Armashin da ke tare da littafin

[gyara sashe | gyara masomin]

Duk da cewa littafin na da matuƙar tsayi, amma hakan bai hana masu bibiyar shi ci gaba da bibiyar sa da kuma neman shi ba, littafin ya tafi tun daga kan littafi na ɗaya har zuwa littafi na biyar. Kana kuma ya ɗora da ci gabansa mai suna Matsatsubi wanda shi ma ya kai har littafi  na huɗu, amma wani abin mamaki har gobe za ka iya ji ana maganar littafin kuma ana neman shi musamman a kafofin sada zumunta. Wannan ya nuna ƙwarewar marubucin tare da nuna yadda ya iya jan zarensa a fagen harkar rubutu

Muhimman jigogin labarin

[gyara sashe | gyara masomin]
  • Babban jigo na labarin shi ne nuna karfin ikon Allah a kan hallita.
  • Sai kuma yaƙi musamman tsakanin garuruwan da suka kasance na Musulmai da kuma Kafurai.
  • Akwai kuma sarauta wadda ta kasance kusan ita ce ƙashin bayan ɗarsa ɗanbar yaƙin.
  • Akwai yaudara da cin amana waɗanda suka kasance sannanun abubuwa da suke gudana a rayuwar gidan sarauta.
  • Haka kuma labarin ya tabo abin da ya shafi tsafi bokanci sa kuma tsantsar sihiri.

Ƙananun jigogi a labarin

[gyara sashe | gyara masomin]

1. Jarumtaka

2. Soyayya

3. Yaudara

4. Cin amana

5. Zalunci

6. Sihiri

7. Hatsabibanci

Wasu muhimman bayanai game da labarin

[gyara sashe | gyara masomin]

Akwai muhimman bayanai masu gamsar da zuciyar mai karatu game da labarin kamar su;

-Tasirin addini Musulunci a kan Kafirci

-Tasirin gaskiya a kan ƙarya

-Tasirin adalci a kan zallunci

Shi ne littafin yaƙi na farko da marubucin ya yi da ya fi sauran littattafansa na baya yawan shafuka

Karɓuwar labarin

[gyara sashe | gyara masomin]

Karɓuwar labarin ba ya rasa nasaba da tsawon labarin da ambaton jinsin aljanu da yawa fiye da kowanne labaransa a lokacin.

Karanta littafin a rediyo wanda hakan ya haddasa yaɗuwar audio nasa a sassan ƙasar Hausa ya janyo masa karɓuwa matuƙa sosai

Har a lokacin makaranta da ma har yau ba su yarda cewa hikimar marubucin ba ce face fim ya juya zuwa littafi.

Kasancewar littafin bai zama mallakin marubucin ta fuskar ɗab’i ba, hakan ya janyo aka kasa kammala buga ƙarshen littafin wato Mifthul-Zarbil na uku (3). Duk kuwa da cewar marubucin ya rubuta ƙarshen labarin.

Hakan ya janyo naƙasu ga marubucin sosai ta fuskar masoya saboda rashin ƙarasa labari da ba ya

Ra’ayoyin jama’a game da labarin

[gyara sashe | gyara masomin]

Dr. Mubarak Idris ya ce:

“Ni dai har yanzu ban samu labarin yaƙi kamar shi ba, kuma ina ganin kamar an gama ƙarar da ƙirƙirar labarin yaƙi a wannan littafin.”

Marubuci Mansur Usman Sufi ya ce:

“Duk da cewar za a samu littattafan marubucin da wasu marubutan da dama da suka yi labari da ya ɗara Kundin Tsatsuba. Amma tabbas ya samu ɗaukakar da babu kamarsa.”

Marubuci Muttaka A Hassan ya ce:

“E, to. Ba lallai na iya faɗar wasu abubuwa muhimmai a kan littafin ba kasancewar ko littafi na farko ban gama karantawa ba na watsar, wataƙila saboda daina karanta littafan yaƙe-yaƙe da tsafe-tsafe da na yi. Amma babu shakka idan na tuna wasu littafai da Abdul’aziz Sani Madakin Gini ya rubuta, sai in ce gwani ne, sannan kuma ɗan baiwa. Ya iya isar da saƙo cikin hikima, musamman yadda ya iya samar da hoto a labari.”

Kamal Muhammad ya ce,

“Yadda aka tsara labarin kaɗai abin armashi ne. Duk da yawansa kuma ba na gajiya da karanta shi. Abin da ya fi burgewa a gare ni yadda yake tsara sunayen bokaye kala-kala da kuma dazuzzuka. Akwai wata bokanya wai ita Samarratu da kuma jaruma Sharmila da boka Markahusabuss abin kam akwai burgewa matuƙa ko da kuwa film ɗin yaki ya juya kamar yadda ake hasashen ya yi rawar gani ya kuma yi ƙoƙari.”

Bayanin littafin a taƙaice

[gyara sashe | gyara masomin]

Marubuci: Abdul’aziz Sani Madakin Gini (Yaron Malam?

Adadin shafuka: 1200

Harshe: Hausa

Maɗaba’a: Jakara City Bookshop

Shekarar ɗab’i: 2006

Karantawa a audio: Muhammad Umar Kaigama

Wajen Wallafa: Kano, Najeriya

Tsara bango: Jakara City Bookshop

ShuraidDev. (2024, November 6)Tarihin Marubuci Abdul’aziz Sani Madakin GiniArewanovels.com

  1. https://bakandamiya.com/kundin-tsatsuba/