Kunun Gyaɗa

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Kunun Gyaɗa ya kuma kasance abin sha ne a ƙasar Hausawa dake yawanci Arewacin Najeriya, wanda ake hada shi da markadadiyar gyada da kuma shinkafa. Kunu ne mai dadin gaske da kauri kuma ana shan shine da zafi zafi.

Kunun Gyada abinci ne na Arewacin Najeriya wanda aka yi da ɗanyen gyada da shinkafa. kamar yadda ake yin Akamu,[1]

[2]

Kayan Hadi[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Gyaɗa
  2. Shinkafa
  3. Ruwa (Sanyi da Zafi)
  4. Tsamiya ko Lemun Tsami

[3]

Kayan Aiki[gyara sashe | gyara masomin]

1. Ana bukatar Abin markade domin markada Gyadar da Shinkafa

2. Ana buƙatar yadin domin tacewa [4]

Yanda ake Hada Kunun Gyada[gyara sashe | gyara masomin]

Kafin a Hada Kunun Gyada Ana bukatar da a jika shinkafar a ruwa a kalla awowi 8, Itama Gyadar tana bukatar a jika ta a ruwa na tsawon awowi 3, Sai a jika Tsamiyar itama a cikin ruwa mai dumi domin tayi laushi kuma ta narke sinadarin dake jikinta, Bayan an jika sai a markada gyadar da ruwa a tace madara, sai a markada shinkafar itamada ruwa daban a mazubi daban. [5]

Matakan Hadawa

1. A zuba madarar gyadar a cikin tukunya a fara dafawa da wuta matsakaiciya, a ringa juyawa da ludayi ko yar sanda ana motsawa sosae har karshen tukunyar idan ba haka ba zai yi kullutai a ciki.

2. Lokacin da ta tafasa, a hankali a zuba markadadar shinkafar anayi ana juya a hankali.

3. Idan ya kara tafasa sai a zuba wuran tsamiyar a ciki anayi ana juyawa.

4. A cigaba da juyawa har ya kara tafasa, sannan sai a zuba a sha cikin aminci.

Ana iya shan kunun gyada mai zafi da kosai ko kuwa a sha shi shi kadai. [6]

Amfani a Jiki[gyara sashe | gyara masomin]

1. Gyada na ƙara girman jikin mutum musamman yara domin yana dauke da sinadarin ‘Protein’.

2. Gyada na gyara fatar jikin mutum da hana saurin tsufa saboda kasancewar sinadarin ‘vitamin E’ a ciki.

3. Gyada na kare mutum daga kamuwa da cutar bugawar zuciya.

4. Gyada na dauke da sinadarin ‘vitamin B3’ wanda ke taimakawa wajen hana mutum mantuwa.

5. Gyada na gyra jiki kuma Tana na Kara kiba.

[7]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]