Kurya Madaro
Kurya Madaro gunduma ce, dake cikin Ƙaramar Hukumar Kaura-Namoda dake a Jahar Zamfara, arewa maso yammacin Nigeria. [1]
Tarihi
[gyara sashe | gyara masomin]Garin Kurya-Madaro an kafa shi bisa turbar Musulunci a karkashin Jagorancin Mujaddadi Shehu Usman Dan Fodio fiye da shekara ɗari biyu da suka wuce.[ana buƙatar hujja]
Asalin suna
[gyara sashe | gyara masomin]An samu sunan wannan gari daga yawaitar itatuwan Kurya shi yasa ake kiranta da sunan Kurya ita kuma sarautar Madaro an same tane sanadiyyar wata rijiya da aka isko mai ruwa kamar Madara,[ana buƙatar hujja] Adamu kada da Ja'oji su suka kafa wannan gari na Kurya Madaro inda babban su Ɗan Abore ya hurce garin Rawayya inda ya kafa nasa gari mai suna Rawayya, dukkansu ƴan ƙabilar Jallawane.[ana buƙatar hujja]
Alh. Mahmud Muhammad Salati shine ubanƙasar Kurya Madaro [2]
Hotuna
[gyara sashe | gyara masomin]-
Fadar uban ƙasar Kurya Madaro
-
Uban ƙasar Kurya Madaro Alh. Mahmud Muhammad Salati Tare da Bashir Madaro Kurya (Walin Kurya) bayan tasowa daga Sallar Idi 2020]]