Jump to content

Kwalejin Ilimi ta Jihar Zamfara

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Kwalejin Ilimi ta Jihar Zamfara
Bayanai
Iri jami'a da school of education (en) Fassara
Tarihi
Ƙirƙira 2000
zcoemaru.edu.ng

Kwalejin Ilimi ta Jihar Zamfara makaranta ce ta gaba da sakandare ta gwamnatin jihar da ke garin Maru a jihar Zamfara, Najeriya .Shugaban makarantar na yanzu shine Ibrahim Usman Gusau.

An kafa Kwalejin Ilimi ta Jihar Zamfara a shekarar 2000. A da ana kiranta da ‘Teachers’ Training College (TTC)’, daga baya kuma aka canza ta zuwa ‘Advanced Teachers’ College (ATC)’ daga baya kuma aka canza mata suna zuwa Kwalejin Ilimi ta Jihar Zamfara.

Cibiyar tana ba da darussa kamar haka;

  • Ilimin Kimiyya
  • Ilimin Halitta
  • Hausa
  • Ilimin Kwamfuta
  • Larabci
  • Geography
  • Ilimin Ingilishi
  • Ilimin Lissafi