Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya, Nekede
Appearance
Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya, Nekede | |
---|---|
| |
Bayanai | |
Iri | polytechnic (en) |
Ƙasa | Najeriya |
Harshen amfani | Turanci |
Tarihi | |
Ƙirƙira | 1978 |
fpno.edu.ng |
Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya, Nekede babbar kwaleji ce mallakar gwamnatin tarayya da ke Nekede, karamar hukumar Owerri West a jihar Imo, Kudu maso Gabashin Najeriya. An kafa ta ne a wani wuri na wucin gadi a harabar Government Technical College ta Jihar Imo a shekarar 1978 a matsayin Kwalejin Fasaha, Owerri kafin a matsar da ita zuwa inda take a yanzu a Nekede. A ranar 7 ga watan Afrilu na shekarar 1993, aka canzawa polytechnic ɗin suna zuwa kwalejin fasaha ta tarayya kuma aka sauya masa suna zuwa "Federal Polytechnic, Nekede". A cikin Federal Polytechnic, Nekede a na bada horon karatu da shaidar National Diploma da Higher National Diploma.
Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.