Jump to content

Kwalejin Koyon Aikin Jinya da Ungozoma ta Jihar Bauchi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Kwalejin Koyon Aikin Jinya da Ungozoma ta Jihar Bauchi
Bayanai
Iri jami'a
Tarihi
Ƙirƙira 2010

Kwalejin koyon aikin jinya da ungozoma ta jihar Bauchi wata cibiyar koyar da ilimin kiwon lafiya ce mallakar gwamnati dake birnin Bauchi, a jihar Bauchi, dake tarayyar Najeriya. [1] Ta fara aiki ne a shekarar 2013 bayan shekaru uku da gwamnatin jihar ta kafata. [2]

Kwalejin tana gudanar da darussa masu alaƙa da lafiya, daga cikinsu akwai:

  • Ilimin Koyon Kula da Majinyata
  • Karatun Aikin Ungozoma
  • Ilimin Kula da Al'umma

Hukumar NMCN ta ba da izini ga kwalejin a cikin 2019. [3]