Wasan ƙwallon ƙafa shi ne mafi shaharar wasanni a Chadi.[1][2][3]Da yawa daga cikin manyan 'yan wasan ƙwallon ƙafa na Chadi sun taka rawar gani a Faransa . A cewar wata majiya mai tushe, Nambatingue Tokomon, wanda aka fi sani da "Toko", ya taka leda a shahararrun ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na Faransa, ciki har da Paris St. Germain, a cikin shekarar 1970s da 1980s. Abdoulay Karateka shi ma ya taka leda a Paris St. Germain. Ndoram Japhet ya taka leda a Nantes da Monaco a cikin shekarar 1990s. Tawagar ta ƙasa tana wakiltar ƙwallon ƙafa a ƙasar Chadi a ƙasashen duniya, duk da haka, tawagar ba ta taɓa samun gurbin shiga gasar cin kofin duniya ta FIFA ko gasar cin kofin ƙasashen Afirka ba. Ba su shiga gasar neman cancantar shiga gasar cin kofin duniya ba sai a shekara ta 2002.