Jump to content

Lanre Okunlola

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Lanre Okunlola
Rayuwa
Haihuwa 26 ga Janairu, 1966 (58 shekaru)
ƙasa Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa

Lanre Okunlola (an haife shi (1966-01-26) ɗan siyasar Najeriya ne kuma ɗan majalisar wakilai na yanzu a majalisar wakilai ta ƙasa ta 10, mai wakiltar mazaɓar Surulere II ta tarayya tun a watan Yuni 2023.[1][2] Shi ne mataimakin shugaban kwamitin majalisar kan bada tallafi, lamuni, da kula da basussuka. Tun lokacin da Lanre Okunlola ya zama ɗan majalisar wakilai ta ƙasa, ya ɗauki nauyin kudirori sama da 12, tare da ɗaukar nauyin wasu da dama, tare da gabatar da kudiri a majalisar wakilai [3]

Rayuwar farko da ilimi

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Lanre Okunlola a ranar 26 ga watan Janairu, 1966 a Lagos, Najeriya, ga Mista da Mrs. Okunola. Ya yi karatun firamare da sakandare a Legas tsakanin a shekarun 1970 zuwa 1980.

A shekara ta 1988, ya sami digiri na farko a fannin gine-gine, daga baya kuma ya sami digiri na biyu a wannan fanni, wanda ya kara karfafa tushe na ilimi da kwarewa a fannin gine-gine.[4][5]

Aikin siyasa

[gyara sashe | gyara masomin]

Lanre ɗan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ne, kuma yana wakiltar mazaɓar tarayya ta Surulere II a majalisar dokokin Najeriya ta 10. An zaɓe shi ne a lokacin babban zaɓen shekarar 2023, inda ya yi nasara da kuri’u 27,725. Okunlola yana aiki a matsayin mataimakin shugaban kwamitin majalisar kan bada tallafi, lamuni da kula da basussuka.[6]

  1. "APC's Lanre Okunlola wins Surulere II in Lagos". Pulse nigeria. 2023-02-27. Retrieved 2024-11-25.
  2. Soyele, Olugbenga. "Tribunal Affirms APC's Reps Victory In Surulere Constituency II". Leadership.ng. Retrieved 2024-11-25.
  3. Sulaiman, Goni. "Bills Sponsored / Co-sponsored by Hon. Lanre Okunlola". Bills Track. Retrieved 2024-11-15.
  4. Sulaiman, Goni. "Bills Sponsored / Co-sponsored by Hon. Lanre Okunlola". Bills Track. Retrieved 2024-11-15.
  5. Goni, Sulaiman (2023-04-21). "Election result: APC's Lanre Okunlola wins Surulere Reps seat". Daily Post Nigeria. Retrieved 2024-11-25.
  6. Sulaiman, Goni (2024-06-20). "Aspirant gives out free 300 JAMB forms". The Nation Online. Retrieved 2024-11-25.