Jump to content

Lazarus Chakwera

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Lazarus Chakwera
Shugaban kasar malawi

28 ga Yuni, 2020 -
Peter Mutharika (en) Fassara
Election: 2020 Malawian presidential election (en) Fassara
Minister of Defence (en) Fassara

28 ga Yuni, 2020 - 31 ga Janairu, 2023
Peter Mutharika (en) Fassara
Member of the National Assembly of Malawi (en) Fassara

2010 -
District: Lilongwe North West (en) Fassara
Election: Malawian legislative election, 2014 (en) Fassara
Rayuwa
Haihuwa Lilongwe, 5 ga Afirilu, 1955 (69 shekaru)
ƙasa Malawi
Karatu
Makaranta Jami'ar Malawi
Jami'ar Limpopo
Trinity International University (en) Fassara
Jami'ar Afirka ta Kudu
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa, Malamin akida da Malami
Imani
Addini Assemblies of God (en) Fassara
Jam'iyar siyasa Malawi Congress Party (en) Fassara

Lazarus McCarthy Chakwera (an haife shi ranar 5 ga watan Afrilu shekarar 1955) ɗan siyasan Malawi ne kuma wanda ya yi aiki a matsayin Shugaban Malawi kuma ministan tsaro tun watan Yunin shekarar 2020.[1] Har ila yau, yana aiki a matsayin ministan tsaro ga kundin tsarin mulkin Malawi, Ya yi aiki a matsayin shugaban jam'iyyar Congress Party daga 2013.[2] Ya kasance Shugaban majalisar Cocin (Assemblies of God) a Malawi daga 1989 zuwa 2013.

A baya, Chakwera shi ne shugaban ƴan adawa a majalisar dokokin kasar bayan zaɓukan da aka gudanar a ranar 21 ga watan Mayun shekarar 2019 da kotun tsarin mulkin kasar ta soke. An nada shi shugaban SADC a ranar 17 ga watan Agusta[3] a taron shekara-shekara na SADC karo na 41 da aka gudanar a ranar 9 ga Agusta zuwa 19 ga Agusta 2021 a Lilongwe, Malawi.

An haifi Lazarus a Lilongwe, babban birnin Malawi, a ranar 5 ga watan Afrilu shekarar 1955 [4] a lokacin da ƙasar ke ƙarƙashin mulkin mallaka na Burtaniya.[5] Mahaifinsa malamin makarantar firamare ne kuma yana samun abin hidima da ciyar da iyalinsa ta hanyar sana'ar noma.[6] Ya auri Monica Chakwera a ranar 8 ga watan Oktoba, shekarar 1977, sun haifa ƴa'ƴa huɗu (namiji ɗaya da mata 3).[7]

Chakwera ya kammala karatun digiri na farko a sashen Arts (Palsapa) daga Jami'ar Malawi a shekarar 1977. Ya karanta ilimin tauhidi sannan ya sami digirin girmamawa a Jami'ar Arewa ta Afirka ta Kudu sannan ya sami digiri na biyu (MTh) a Jami'ar Afirka ta Kudu a 1991.[7] Jami’ar Trinity International da ke Amurka ta ba shi digirin digirgir (D.Min) a shekarar 2000. Ya zama farfesa a Makarantar Pan-Africa Theological seminary a 2005.[5]

Aikin Tauhidi na coci

[gyara sashe | gyara masomin]

Ya yi aiki a matsayin malami a (Assemblies of God) daga 1983 zuwa 2000 inda ya zama Shugaban Makarantar a 1996. Ya kasance babban darekta kuma malami a Makarantar Tauhidin kiristanci ta Duniya.[8] Daga 1989 zuwa 2013 ya jagoranci Majalisar Malawi ta Ubangiji.[8] A ranar 14 ga Afrilu 2013 ya ba wa mutane da yawa mamaki lokacin da ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takara a babban taron jam'iyyar adawa ta Malawi Congress Party (MCP) a matsayin shugaban kasa yayin da yake ci gaba da rike Majalisar Dokokin ubangiji.[9]

  1. "Lazarus Chakwera sworn in as Malawi president after historic win". BBC News. 28 June 2020. Retrieved 28 June 2020.
  2. Welle (www.dw.com), Deutsche. "Who is Malawi's new leader Lazarus Chakwera? | DW | 27.06.2020". DW.COM (in Turanci). Retrieved 2021-01-11.
  3. "Southern Africa: SADC to Hold 41st SADC Summit in Malawi". allAfrica.com (in Turanci). 2021-08-09. Retrieved 2021-08-20.
  4. "Curriculum Vita: Lazarus M. Chakwera, BA, BTh (Hons), MTh., D.Min" (PDF). Wise One From The East. Archived from the original (PDF) on 5 October 2013.
  5. 5.0 5.1 "Man of God, Welcome to Cut Throat Politics". Zodiakmalawi.com. 17 April 2013. Archived from the original on 30 June 2013. Retrieved 3 October 2013.
  6. "Personal Story of Lazarus Chakwera : AGTV". Agtv.ag.org. 24 June 2010. Retrieved 3 October 2013.
  7. 7.0 7.1 "Malawi on the road to 2014: Rev. Dr. Lazarous Chakwera". Nyasa Times. 15 April 2013. Archived from the original on 4 March 2016. Retrieved 3 October 2013.
  8. 8.0 8.1 "On the Road to 2014: Dr. Lazarus McCarthy Chakwera". Malawi Voice. Archived from the original on 4 October 2013. Retrieved 3 October 2013.
  9. "Chakwera guns for MCP presidency". Archived from the original on 16 May 2013. Retrieved 22 April 2013.