Lily Tembo

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Lily Tembo
Rayuwa
Haihuwa Kabwe (en) Fassara, 20 Nuwamba, 1981
ƙasa Zambiya
Mutuwa Lusaka, 14 Satumba 2009
Yanayin mutuwa  (gastritis (en) Fassara)
Karatu
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a ɗan jarida

Lily Tembo (Nuwamba 20, 1981 - Satumba 14, 2009), wacce aka fi sani da Lily T, mawaƙiyar Zambiya ce, mai gabatar da shirin rediyo, ƴar jarida kuma ma'aikaciyar agaji[1][2] wacce ta sami yabo ta ƙasa tare da kundi na farko na 2004 Lily T.[3] Dalilin wannan kundin, ta sami kyaututtuka biyu.

Tembo ta saki albam guda biyu kuma tana aiki akan na uku a kafin mutuwarta. Baya ga waƙa, ta shahara wajen gabatar da shirye-shirye a gidan rediyon 5th FM a ƙasar Zambiya, inda ta yi aikin jarida da kuma ayyukan agaji.

Tarihin rayuwa[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Tembo a Kabwe, Zambia, kuma ta girma a cikin iyali masu son kiɗa. Mahaifinta, ya buga wasan bongo na Afirka, haka-zalika yayyenta da mahaifiyarta, sun rera waƙa a coci. Tembo ta halarci makarantar sakandare a makarantar sakandare ta ƴan mata ta Kabulunga da ke a Lusaka, babban birnin kasar Zambia. Daga baya, ta ci gaba da aikin jarida a Kwalejin Evelyn Hone.

Tembo ta shiga sabgar waka a shekara ta 2004 tare da fitar da album dinta Mai taken: Lily T, wanda shine dalilin fara sana'arta ta waƙe, kuma ya jawo hankalin ƙasar ta, akanta.[3] Ta fitar da kundi na biyu a shekara ta 2006. Tembo ta kasance mai karanta labarai na gidan rediyon 5th FM, da ke Lusaka, Zambia.

Bayan lashe lambar yabo guda ɗaya, BBC Africa ta karɓe ta a matsayin fitacciyar jarumar Afirka wacce ta kasance ta asali ga kayan gargajiya.

Aikin sadaka[gyara sashe | gyara masomin]

Lily ta taka rawa wajen wayar da kan jama'a akan cutar zazzabin cizon sauro a Zambia. A watan Afrilun 2009, ta jagoranci masu ibada a taron tunawa da ranar zazzabin cizon sauro na duniya a birnin Lusaka.[4]

Albam[gyara sashe | gyara masomin]

  • Lily T (2004)
  • Osalila (2006)

Kyaututtuka da ayyanawa[gyara sashe | gyara masomin]

Shekara Kyauta Iri Sakamako
2005 Koala Awards Best New Artist Nominated
2007 Ngoma Awards Best Female Recording Artist Nasara
Best Music Video Award Nasara

Mutuwa[gyara sashe | gyara masomin]

Bayan ta yi magana game da " ciwon cikin da ke damunta"[5] da fama da matsanancin ciwon ciki,[6][7] Tembo ta mutu a ranar 14 ga Satumba, 2009, tana da shekaru 27 a duniya.

Kafin nan[gyara sashe | gyara masomin]

Ƴar'uwar Tembo Patience ta shaida wa manema labarai cewa "Tana da ciwon ciki, ta kamu da rashin lafiya ranar Asabar, ta fara amai da yawa kuma ta kamu da rashin lafiya. A ranar Litinin da misalin karfe 19:00, ta ce ga garinku nan-(ta mutu)."[8]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Lily Tembo Archived 2018-06-30 at the Wayback Machine Stans Music
  2. Almbum Review: Lily T BH magazine Archived ga Janairu, 6, 2009 at the Wayback Machine
  3. 3.0 3.1 African Entertainment and Music Lyrics Africa Archived ga Yuli, 14, 2011 at the Wayback Machine
  4. World Malaria day Parth Archived Nuwamba, 21, 2009 at the Wayback Machine
  5. Lily Tembo is dead Archived 2014-08-26 at the Wayback Machine UKZambians,(content encoded by Zend Guard)
  6. Zambias female singer Lily T dead AfricaNews Archived Satumba 28, 2011, at the Wayback Machine
  7. [1] Lusaka Times
  8. aaaaaia.com/content/view/13658/50/ Singer Lily T dies The Post Archived Satumba 23, 2009, at the Wayback Machine