Linda Spilker

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

  Linda Spilker it's din wata ƙwararriyar yar kimiya ce ta duniya wacce ta yi aiki a matsayin ƙwararren masaniyar kimiyyar aikin Cassini da ke binciken duniyar Saturn . Abubuwan bincikenta sun haɗa da juyin halitta da haɓakar zoben Saturn.

Sana'a[gyara sashe | gyara masomin]

Spilker ta sami B.A.in Physics daga Jami'ar Jihar California, Fullerton a cikin shekara 1977 da MS a cikin Physics daga Jami'ar Jihar California, Los Angeles a 1983. Ta samu Ph.D. a cikin Geophysics da Space Physics daga UCLA a cikin shekara 1992. Ta shiga dakin gwaje-gwaje na Jet Propulsion Laboratory a shekara 1977, da farko tana aiki a kan ayyukan Voyager da aka kaddamar a wannan shekarar. Ta zama masaniyar kimiyar Cassini shekara 1990. A cikin shekara 1997, ita ce editan littafin NASA wadda ta taƙaita abubuwan da aka daga manufarta. A cikin shekara 2010 ta zama masaniyar kimiyyar aikin Cassini, rawar da ta jagoranci duk binciken kimiyyar ƙungiyar. Ta fito a matsayin kanta a cikin shirye-shiryen talabijin da yawa, gami da da yawa a cikin jerin PBS Nova.

Girmamawa da kyaututtuka[gyara sashe | gyara masomin]

  • Medal na Musamman na NASA shekara (2013)
  • Kyautar Nasarar Ƙungiya ta NASA shekara (2011, 2009, 2000, 1998, 1982-1989)
  • Kyautar Nasarar Kimiyya ta NASA shekara (1982)

Duba kuma[gyara sashe | gyara masomin]

  • Jerin mata masu matsayi na jagoranci akan ayyukan kayan aikin taurari

Nassoshi[gyara sashe | gyara masomin]