Jump to content

Maƙabartar Wadi-us-salam

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Maƙabartar Wadi-us-salam
Islamic cemetery (en) Fassara
Bayanai
Farawa 1873
Suna a harshen gida وادي السلام
Addini Musulunci
Ƙasa Irak
Heritage designation (en) Fassara Tentative World Heritage Site (en) Fassara
World Heritage criteria (en) Fassara (iii) (en) Fassara, (v) (en) Fassara da (vi) (en) Fassara
Wuri
Map
 32°00′18″N 44°18′54″E / 32.005°N 44.315°E / 32.005; 44.315
Ƴantacciyar ƙasaIrak
Governorate of Iraq (en) FassaraNajaf Governorate (en) Fassara
BirniNajaf

Maƙabartar Wadi-us-salam Maƙabarta ce ta Musulmai, da ta ke a birnin Najaf, a ƙasar Iraq. Maƙabartar itace mafi girma a dunia.[1][2] Tana da girma daya kai 1,485.5 acres (601.16 ha; 6.01 km2; 2.32 sq mi) sannan tana dauke da mutanen da aka rufe sama da miliyan shida.[3]. A duk shekara miliyoyin mutane ne suke zuwa ziyara a wannan Maƙabarta.

Maƙabartar Wadi-us-salam, tana kusa da haramin Aliyu Ibn Abi ɗalib (a.s), wato imami na farko bayan manzon Allah a wurin shi'a, haka zalika khalifa na hudu bayan manzon Allah a Sunni.[4] yan shi'a da yawa dake a kasar Iraq suna kwadayin ƙabarin su ya kasance a wannan maƙabarta. Maƙabartar ta samu ci gaba sosai ta bangaren sufuri, kuma mabiya shi'a da dama a fadin duniya suna bada wasiyya a rufesu a can bayan mutuwar su.

An aerial view of Wadi-al-Salam cemetery


Mahangar shi'a akan maƙabartar

[gyara sashe | gyara masomin]
Maqam al-Mahdi in Wadi-us-salam

Shi'a sunyi riko da cewa Annabi ibrahim (a.s), shine wanda ya assasa/ya kawo maƙabartar wadi-us-salam , a lokaci an ruwaito cewa imam Ali yace maƙabartar ta wadi-us-salam wani yanki ne daga cikin aljanna.[5] Kuma mabiya shi'a sunyi imani da cewa mutanen dake kwance a wannan maƙabarta suna samun sausauci daga ubangiji kasancewar su maƙwabtan imam Ali (a.s)[6] za'a tashe su a tare a ranar alikiyama.

Tahiri ya tabbatar da cewa an fara rufe mutane a wannan maƙabarta sama da shekara dubu daya da dari hudu da suka gabata. kuma hakan ya samo asali tun daga daular Parthian, Sassanid, da kuma yankunan da ake kira da Mesopotamian.kuma duka wadannan dauloli da yankuna sunada maƙabartu kusan iri daya saboda sunda ƙaburbura masu daki daya (abinda ake kira da ingilishi tombs)[7]

Masu ƙididdiga tun sun ruwaito ana rufe mutum 200 zuwa 250, a lokacin yakin Iran da Iraq. Amma a shekarar 2010 adadin ya ragu zuwa mutum dari a rana.[8] A takaice an kiyaye ana kimanin mutum dubu a shekara daga sassan duniya.[9]

Wurare masu daraja

[gyara sashe | gyara masomin]

Shahararrun jana'iza

[gyara sashe | gyara masomin]

A wannan maƙabarta rufe manyan mutane da suka shahara, wadanda suka hada da

  1. https://books.google.com.ng/books?id=Q_-hrXU-mWYC&pg=PA140&redir_esc=y#v=onepage&q&f=false
  2. The world's biggest cemetery". BBC News. 2016-06-12. Archived from the original on 2021-04-16. Retrieved 2022-06-27.
  3. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2016-03-26. Retrieved 2023-03-07.
  4. "Najaf cemetery witness to Iraq's tragic history - USATODAY.com
  5. Dumper, Michael; Stanley, Bruce E., eds. (2007). Cities of the Middle East and North Africa: A Historical Encyclopedia (illustrated ed.). ABC-CLIO. p. 269. ISBN 9781576079195. There is also the tradition that Abraham bought land in the Wadi as-Salaam (Valley of Peace) that runs through the present city, predicting that it would be from here that 70,000 of those buried in the valley would be guaranteed entrance into paradise and would then be able to intercede with Allah for others. Imam Ali is reported to have said that Wadi as-Salaam was a part of heaven.
  6. Yasser Tabbaa; Sabrina Mervin (28 July 2014). Najaf, the Gate of wisdom. UNESCO. pp. 162–3. ISBN 9789231000287
  7. Yasser Tabbaa; Sabrina Mervin (28 July 2014). Najaf, the Gate of wisdom. UNESCO. p. 162. ISBN 9789231000287. Such burial sites are quite common in ancient Mesopotamian cities, where the accumulation of tombs has created mounds on the outskirts of these early settlements
  8. "Najaf cemetery witness to Iraq's tragic history - USATODAY.com". usatoday30.usatoday.com. Archived from the original on 2014-11-30. Retrieved 2022-06-27.
  9. Wadi al-Salam: The world's largest cemetery". Al Jazeera.