Jump to content

Magajiya Danbatta

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Magajiya Danbatta
Rayuwa
ƙasa Najeriya
Mutuwa Dambatta, Oktoba 2021
Sana'a
Sana'a mawaƙi

Magajiya Dambatta ko Danbatta ƴar asalin garin Dambatta ce a Jihar Kano, shahararriyar mawaƙiyar Hausa ce wacce ta samar da waƙoƙi na shawarwari masu yawa a cikin shekarun 70 kan mahimmancin ilimi, kyawawan dabi'u, da tarbiyyar yara, yayin da kuma take tir da munanan halayen jama'a, da sauransu.[1]

Tarihi[gyara sashe | gyara masomin]

Mawaƙiya Magajiya Danbatta wadda asalin sunanta shine Halima Malam Lasan, an haife ta ce kimanin shekara 84 ko 85 da suka gabata, wannan zabiyat ta yi tashe da shahara sosai, inda ta kasance cikin mawaƙa manya da duniyar Hausa ke sauraro kuma suka yi takama da su a tsakanin shekarun 1970 zuwa 1980. Bayan dogon lokaci tana tashe, sai kwatsam ta yi batar dabo, inda aka daina jin duriyarta, waɗanda suka santa kuma suka manta da ita, matasa kuma da ma can ba su santa ba. Magajiya Ɗanbatta ta fara waƙa ne tun tana da shekaru 12, kuma ta yi waƙoƙi da dama inda ta shahara a wancan lokaci ta yadda idan ba ta je taro ta yi waƙa & ba, taron bai cika yin dadi ba. Ta ce sun hadu da Shata a lokacin bikin cikar Gidan Rediyon Najeriya Kaduna shekara 30, inda ta rera wakarta mai suna Soriyal.

Bayan dogon lokaci, sai kwatsam a ranar 23 ga Disamban shekara ta 2019, dan jarida Jafar Jafar ya wallafa wani faifan bidiyo na Magajiya Dambatta na wakar da ta yi a Gidan Rediyon Najeriya Kaduna na bikin cika shekara 30.[2] Wannan ya jawo hankalin mutane daga Arewacin Najeriya musamman ma matasa. Bayan gano Magajiya Ɗanbatta ta makance sai ɗan jarida Jafar Jafar ya yi kira ga mabiyansa a shafukan sada zumunta da cewa su haɗa gidauniya domin tara kuɗi saboda tallafawa Magajiya Ɗanbatta. Kiran ya samu karɓuwa sosai inda aka tattara ƙudade masu dama kuma aka tallafa mata.[3][4][5]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. https://m.youtube.com/watch?v=VsWsUIQSBO0
  2. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2020-11-29. Retrieved 2020-11-04. More than one of |archiveurl= and |archive-url= specified (help); More than one of |archivedate= and |archive-date= specified (help)
  3. https://prnigeria.com/2019/12/24/dambatta-philanthropist-pledges-rehabilitate/
  4. https://hausa.legit.ng/1289947-dare-daya-allah-kanyi-bature-mutane-sun-hadawa-magajiya-danbatta-taimakon-naira-miliyan-5-sanadiyyar-jaafar-jaafar.html
  5. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2021-02-26. Retrieved 2020-11-04. More than one of |archiveurl= and |archive-url= specified (help); More than one of |archivedate= and |archive-date= specified (help)